Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Ba Da Belin Dan Canjin Kudi Mustapha Naira


Kasuwar canji a Abuja, Najeriya
Kasuwar canji a Abuja, Najeriya

Samame a kasuwar canjin ya haddasa sanya wasu ‘yan kasuwar buya inda har ta kai ga EFCC ta kama wasu daga cikin ‘yan kasuwar amma daga bisani ta sake su.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta ba da belin dan canjin kudi a kasuwar canji ta Abuja Muhammad Adam Almustapha da a ka fi sani da Mustapha Naira.

EFCC dai ta kama Mustapha Naira bisa zargin ya furta kalaman da ke neman ta da farashin dala a daidai lokacin da Naira ta samu koma bayan da ba ta taba samu ba a tarihi.

Samame a kasuwar canjin ya haddasa sanya wasu ‘yan kasuwar buya inda har ta kai ga EFCC ta kama wasu daga cikin ‘yan kasuwar amma daga bisani ta sake su.

Alh.Yahaya Jidda Kida
Alh.Yahaya Jidda Kida

Gabanin yayata wani labarin marar tushe da ke cewa Amurka ma ta shirya canja kudi da daina karbar takardar da a ka buga kafin 2021, kasuwar canjin ta tumbatsa da masu sayan dala don boye makudan kudinsu na Naira da gujewa zuwa banki kar su fada tuhuma daga EFCC; hakan ya cilla dala har fiye da Naira 900.

Tsohon shugaban kasuwar canjin Alhaji Salisu Garu na daga wadanda suka karbo belin Mustapha Naira wanda EFCC ke son gani lokaci-lokaci kafin shafa ma sa lafiya.

Alhaji Salisu Garu
Alhaji Salisu Garu

Sakataren kwamitin dattawan kasuwar canjin Alhaji Yahaya Jidda Kida ya ce ba sa zagon kasa ga tattalin arziki kuma su na mara baya ga sauya fasalin kudi amma ya na da kyau a yi la’akkari da al’ummar karkara.

Dalar dai ta fara murmurewa daga fadowa da ta yi da kusan Naira 25; kazalika dalar ba ta samuwa yanda a ka saba a bankuna sai an yi ta je-ka-ka-dawo.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:

EFCC Ta Ba Da Belin Dan Canjin Kudi Mustapha Naira - 2'53"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG