Mataimakin babban konturolan hukumar mai kula da shelkwatar hukumar ACG Muhammad Abba Kura ya bayyana haka a zantawa ta musamman.
Muhammad Kura ya kara da cewa a bara hukumar ta tara kudin shiga fiye da ma abun da a ka tsara za ta tara da rarar sama da Naira biliyan 100.
ACG Kura ya ce su na fatan kafin karshen watan nan na Disamba za su kammala tara kudin duk da kalubalen na yakin Ukraine tun da sun yi nisa a tara kudin.
Kura ya bukaci duk ‘yan kasuwa da ke shigo da haja daga ketare su tabbatar su na biyan kudin harajin kaya don nuna kishin kasa da kuma kauce wa matakan hukumar da za ta kai ga asarar kayan.
‘Yan kasuwa musamman na motoci da harajin ya yi wa yawa sun ce yanzu kudin motoci ya ninka don jibgin haraji da faduwar darajar Naira.
Muhammad Buhari na kamfanin MBS MOTORS ya ce hukumar kwastam ba ta wani sassauci don abun da ta ke la’akari da shi, shi ne tara kudi ga gwamnati tun da an samu koma baya daga kamfanin fetur na NNPC.
Har yanzu kwastam na nanata cewa haramun ne shigo da shinkafa daga ketare don karfafa amfani da ta gida; amma hakika ta gidan da a ke magana sai gidan wane da wane don akasarin talakawa ba sa taya ko farashin shinkafar.
Saurari cikakken rahoton a sauti: