A yanzu haka dai kamfanin samar da hasken lantarki na Abuja wato AEDC ya katse wutar lantarki a wasu ofisoshin gwamnatin jihar a ciki harda ofishin sakataren gwamnatin jihar,
A ci gaba da tabbatar da kwanciyar hankali da shugabannin al'umma ke yi albarkacin lokacin da ake ciki na yawaita ayyukan alkhairi, wasu magabata na wata hobbasa ta sake hade bangarorin kungiyar Izala ta Najeriya wuri guda.
'Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da bayyana matsayinsu na shiga takarar neman mukamai daban-daban a babban zaben kasar dake tafe a shekara ta 2023.
An shafe kimanin shekaru 4 da zamansa garin Phata-Kacha dake yankin karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja kango, tun bayan da wani rikicin neman mallakar fili tsakaninsu da mutanen garin Kacha yayi sanadiyyar tarwatsa kauyen.
A jihar Nejan Najeriya dubban 'yan gudun Hijira ne da 'yan bindiga suka raba da muhallansu ke cikin wani mawuyacin hali a wannan wata na Ramadana.
Masu aikin ceto na can na neman wasu mutane da ba a tantance yawan su ba da wani jirgin ruwan kwale kwale ya kife dasu a jihar Neja.
Hukumomi a jihar Kogin Najeriya na gudanar da bincike akan wasu matasa da ake zargin ‘yan kungiyar matsafane da suka addabi birnin Lokoja fadar gwamnatin Jihar.
Shirin dai a karkashin hukumar nan ta kula da tasoshin samar da wutar lantarki a Najeriya wato HYPADEC zai horar da matasan da suka kammala karatunsu na boko amma kuma ba su da aikin yi da hakan zai taimaka wajen rage aikata miyagun ayyuka a kasa.
Gamayyar Jami’an tsaron Nigeria sun samu nasarar tarwatsa wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a wani ofishin ‘yan sanda na jihar Nejan Najeriya.
Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani babban jami’in ‘yan sanda wato DPO tare da wasu jami’an tsaro guda takwas a jihar Neja dake Arewacin Najeriya.
Bayanai dai sun nuna cewa a yanzu haka akwai daruruwan garuruwa da suka zama tamkar kufai a wasu yankuna na kananan hukumomin Rafi, da Shiroro, da kuma karamar hukumar Mariga.
Rahotanni na nuni da cewa, wasu bama bamai da ake zaton mayakan kungiyar Boko haram ne suka binne akan hanyar zuwa garin Galadiman Kogo ta yankin karamar hukumar Shiroro sun tarwatse su ka kashe jami'an tsaro.
Sai dai jam'iyyar ta APC ta ce wannan zargi da jam'iyyar ta PDP mai adawa ta yi ba shi da tushe.
Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro musamman a arewa maso yammaci da gabashin kasar.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Nejan Nigeria ta nuna damuwa matuka akan yadda ‘yan fashin daji ke ci gaba da hallaka jama’a a sassa daban daban na jihar.
Akalla mutum shida ne suka mutu a sakamakon wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar Nejan dake Arewacin Najeriya.
Sakataren gwamnatin jihar Nejan Alh. Ahmed Ibrahim Matane ya ce ba su da labari kan lamarin makafin.
Rahotanni daga jihar Nejan Najeriya na nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai harin da ya hallaka akalla mutum 8 tare da yin garkuwa da wasu da dama a jihar.
Masana da masu sharhi akan sha’anin ilimi a Najeriya na ci gaba da yin sharhi akan yadda karancin Malaman dake koyarwa a Jami'o'n kasar ke kawo cikas wajan samun ilimi mai zurfi.
Jagorar jam’iyyar APC a Nigeria Bola Ahmed Tinibu kuma mai neman tsayawa takarar shugaban kasa karkashin tutar jam'iyar a shekara ta 2023, ya kai zayarar jaje a jihar Neja a sakamakon matsalar bala’in ‘yan fashin daji da suka addabi jihar.
Domin Kari