NIGER, NIGERIA - Bayanai dai sun nuna cewa kimanin mutane 3500 ne da akasarinsu manoma ne da kuma sana’ar kamun kifi ke zaune a garin da ya share kimanin shekaru 200 da kafuwa kafin wannan tashin hankali na shekara ta 2018 ya tarwatsa garin mai hanyar jirgin kasa a bakin kogin Kwara.
A yanzu dai mutanen garin na Phata-Kacha na bukatar sanya hannun gwamnatin jihar Neja domin sake tsugunnar das u ta yadda za su koma rayuwarsu ta da wato aikin noma da kamun kifi.
Malam Ndatsu Abdulmalik daya daga cikin shugabannin al’ummar Phata-Kachan, ya ce a yanzu mutanensu na tarwatse a wasu garuruwa domin neman mafaka.
Mai magana da yawun sarkin Kacha, Alhaji Baba Adamu Umar Sheshi, dan majalisa Abubakar Kacha ya bayyana cewa, ba bu wata matsalar da za ta hana al'ummar komawa garin su na asali.
Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tana fatar samun maslaha a tsakanin bangarorin guda biyu domin gudun komawa ‘yar gidan jiya a cewar sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: