Shirin dai a karkashin hukumar nan ta kula da tasoshin samar da lantarki a Najeriya wato HYPADEC zai horar da matasan da suka kammala karatunsu na boko amma kuma ba su da aikin yi da hakan zai taimaka wajen rage aikata miyagun ayyuka a kasa.
Da yake kaddamar da shirin, sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha wanda Ministan Matasa da wasanni na Najeriya, Sunday Dariye ya Wakilta yace matasan su ne kashin bayan ci gaban kasa, saboda haka dole ne su basu Muhimmanci.
Ya kara da cewa “ba mu da zabin da ya wuce mu karfafa su domin samun ingatacciyar kasa abin dogaro anan gaba,”
Mataimakin Gwamnan Neja, Alh. Ahmed Muhammad Ketso, wanda ya wakilci Gwamnan Neja a taron, ya ce wanan mataki zai rage yawan dogaro da ayyukan gwamnati.
Babban Manajan Hukumar ta HYPADEC, Abubakar Sadiq Yelwa yayi karin haske da cewa bayan sun kammala horar da wadannan matasa 5000 za su debo wasu kuma sannan za a rika basu wasu kudade na alawus.
Wasu daga cikin matasan da suka fito daga jihohin Neja, Kogi, Kwara, Filato, Benue, da kuma jihar Kebbi sun bayyana farin cikinsu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: