Al'amarin da ke matukar bukatar kulawar hukumomi da shugabannin siyasa da sauran masu hannu da shuni.
Malam Kabiru Barde na daya daga cikin 'yan gudun hijirar da ke sansaninsu na garin Gwada ta yankin karamar hukumar Shiroro inda ya ce abincin da za su ci ya kan yi masu wahala a wannan lokaci na azumi.
Sai dai a wannan yanayi ne dai wani dan tallafawa al'uma, Hon. Idris Malagi ya mikawa Gwamnatin jihar Nejan gudummuwar tirela guda na kayan abinci domin mika su ga 'yan gudun hijirar.
Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tallafin ya zo daidai lokacin da ake bukatar shi, in ji shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Nejan, Alh. Ibrahim.
A halin da ake ciki dai akwai daruruwan garuruwan da babu kowa a wasu kananan hukumomi da 'yan bindigar suka tarwatsa a jihar Nejan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: