Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: 'Yan Siyasa Na Ci Gaba Da Bayyana Aniyarsu Ta Neman Mukamai A Babban Zaben Badi


Sanata Aliyu Sabi Abdullahi
Sanata Aliyu Sabi Abdullahi

'Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da bayyana matsayinsu na shiga takarar neman mukamai daban-daban a babban zaben kasar dake tafe a shekara ta 2023.

Wani abu dake daukar hankali matuka shi ne yadda masu rike da mukaman siyasar a yanzu ke kokarin inda za su sake makalewa a jirgin siyasar na shekarar badi.

A jihar Neja alamu na nuna cewa za a yi karon batta a tsakanin gwamnn jihar Alh. Abubakar Sani Bello da kuma dan majalisar dattawan Nigeria, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi.

Domin kuwa a yanzu haka kowa ne daga cikinsu ya nuna bukatarshi na cewa lallai wannan kujera ta Sanata daga arewacin jihar Nejan ya ke bukata a zaben na badi.

"Ni dai na shirya, bisa bukatar al'umman da na ke wakilci, in lokaci ya yi na sayan form din, zan shiga cikin takara." In ji Sanata Aliyu Sabi Abdullahi a zantawarsa da Muryar Amurka ta yi da shi.

Shi ma Gwamna Abubakar Sani Bello ya shedawa magoyansa aniyarsa ta neman wannan kujera.

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

Tuni dai magoya baya suka fara bayya ra'ayinsu akan wannan al’amari inda yayin da wasu ke nuna goyon bayan Sanata Aliyu Sabi Abdullahi wasu kuwa Gwamna Sani Bello suke muradin ganin ya hau kujerar.

A yanzu dai lokaci ne zai nuna yadda zata kaya a tsakanin wadannan jiga jigai na jam’iyyar APC mai mulki a yanzu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
XS
SM
MD
LG