Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabanni A Jihar Neja Sunyi Amfani Da Bukin Karamar Sallah Wajen Neman Zaman Lafiya


Shugabannin al'umma
Shugabannin al'umma

Shugabanni a jihar Nejan Najeriya sun yi amfani da bukukuwan karamar sallah wajen tunatarwa akan muhimmancin zaman lafiya da neman sauki akan matsalar 'yan bindiga da suka addabi jihar.

Jihar Nejan dai na daya daga jihohin Arewacin Najeriya dake fama da wannan Matsalar ta ƴan bindiga, Mai Martaba Sarkin Kagara Alh. Ahmed Garba Attahiru na biyu, yace bayan masarautar ta sha ukubar ƴan bindiga, a yanzu an dan samu natsuwa a sakamakon sabbin matakai da hukumomi suka ɗauka.

Shima dai Mai Martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alh. Muhammad Barau Mu'azu na Biyu yayi kira ga al'ummar Masarautar akan zaman lafiya.

Gwamnan Jihar Nejan Alh. Abubakar Sani Bello da ya gudanar da sallar idin a garin Agaie yace yana fatar samun saukin matsalar ƴan bindiga a jihar Neja.

Wasu shugabannin addinai sun yi amfani da bukukuwan sallar wajen yin kira akan sabinta katin zaɓe domin tunkarar zaɓen baɗi.

Bayan tsaurara matakan tsaro dai a sassa dabam-dabam na Jihar, rahotanni sun nuna cewa an gudanar da bukukuwan lafiya, sai dai ɗan rashin kuzari na rashin nauyin aljihu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG