Garin Tungar Mgajiyar ainihin garin Deborah Samuel dalibar kwalejin ilimi ta Shagari a jihar Sokoto ne wadda wasu matasa suka aika ta lahira bayan da akayi zargin tayi batanci ga Addinin Musulunci a cikin Makon jiya,
Dagacin garin na Tungar Magajiya ENGR.Jafar Muhammed Aliyu Hakimi yace basu ji dadin aukuwar lamarin ba kuma basu goyon bayan amsa tayin da aka yi mashi na komawa jihar Rivers. Bisa ga cewarshi da yake ba a jihar Naija ko garin Rijau lamarin ya faru ba, bai kamata su bar al'ummar da su ke zaune lafiya zuwa wani wuri ba.
A yanzu dai karamar hukumar ta Rijau ta dauki mataki na sanya idanu ga masu yada labaran karya a kafafen sadarwa na zamani akan wannan al'amari inji shugaban karamar hukumar ta Rijau Hon.Bello Baƙo Galadiman Tungan Mgajiya.
A hirar su da Muryar Amurka, iyayen marigayiyar Deborah Samuel sun bayyana cewa, sun mika al'amari ga Allah, saboda haka ba su jayayya da kowa.
A nasu bayanann, shugabannin addinai sun ce suna kokarin kwantar da hanklin jama'a akan lamarin.
A yanzu dai komi na tafiya lami lafiya a tungar Magajiyar tun bayan da aka gudanar da jana'izar.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti: