Rundunar sojin Najeriya ta ce tana aiki tukuru wajen bin umurnin shugaban kasa na kawar da ayyukan ‘yan ta'adda a ko'ina cikin fadin kasar.
Sakacin gwamnati da al'ummar Najeriya na daga cikin abubuwan da suka kawo bazuwar matsalolin rashin tsaro a Arewa maso Gabas da sauran wurare daban daban.
Dubban ‘yan Najeriya marasa lafiya ne ke cikin adadin marasa lafiya miliyan daya da rabi daga kasashe 42 da ke cin gajiyar ayyukan kula da lafiya kyauta daga likitocin da ke yawo kasashen duniya don bayar da agajin kiyon lafiya.
Yayin da wasu kasashen duniya ke fuskantar kalubale ta fuskoki daban-daban, masana sun ce akwai mafita ga kowane irin kalubale da ake fuskanta a duniya.
Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi ta dira kan wasu wuraren shan miyagun kwayoyi ,ta kama matasa maza da mata da yawan su ya kai 28.
‘Yan Najeriya na ci gaba da yin tsokaci akan bukatar mahukunta su rika sanya ido da tabbatar da yin adalci ga dukkan abubuwan da ke faruwa domin kauce wa ci gaba da haifar da matsalolin tashin hankali a kasar.
Hadarin kwale-kwale na ci gaba da lakume rayukan jama'a a Najeriya duk da matakan da mahukunta ke shan alwashin dauka na kawar da aukuwarsu ko magance mace-mace idan aka samu hadarin.
Masu lallura ta musamman sun ce suna fuskantar kalubale wajen tafiyar da lamurran su na yau da kullum saboda rashin kulawa da hakkoki na inganta jin dadinsu.
Masana lamurran tsaro a Najeriya na ci gaba da tsokaci akan yadda ‘yan ta'adda da ake kamawa ke nuna gadara suna bayyana ta'addancin da suka yi, bayan sun shiga hannun hukuma, abinda suke gani da cewa akwai ayar tambaya a ciki.
Yayin da harkokin siyasa suka kankama gadan-gadan a Najeriya, wasu ‘yan kasar na mamakin yadda gwamnatocin siyasa da suka yi mulki suka kasa warware matsalolin rayuwa ga jama'a, tare da nuna fargabar kada gwamnati mai zuwa ta bi sawun ta baya.
A Najeriya, yayin da wasu mayakan kasar ke fagen daga suna fafatawa da abokan gaba, wasu suna can hannu suna fuskantar shari'a akan wasu laifuka da ake tuhumar su akai.
Masana a Najeriya na ganin daga cikin illolin da rashin tsaro ya haifar ga jama'a akwai rashin sanin makomar kananan yara dake gudun hijira, wadanda basu samun ilimi, wanda zai sa su kasance da tsarin rayuwa idan sun girma.
Yayin da shugabannin kasashen duniya ke ci gaba da tsokaci akan yakin da kasar Russia ke yi da Ukraine, Malaman addini sun soma karkata hankulansu akan bukatar jama'a su bada tasu gudunmuwa wajen kawo karshen yakin.
A wasu sassan Najeriya matsalar tsaro na ci gaba da hana jama'a barci da ido biyu rufe, duk da cewa rahotanni na nuna jami'an tsaro na samun galaba akan ‘yan ta'adda a wasu wurare.
A yau Laraba 28 ga watan Satumba aka fara yakin neman zaben 2023 a hukumance a Najeriya.
Masana a Najeriya na ci gaba da cewa rashin karfafa ayyukan jami'an kula da tsaftar muhalli ne abin da ke ci gaba da yin barazana ga samun kyakkyawan muhalli da kuma ingantattar lafiya ga al'ummar kasar.
A Najeriya mata ‘yan siyasa sun ce irin sunayen ‘yan takara da hukumar zabe ta fitar ya kara jefa fargaba cikin zukatansu ganin har yanzu ba a shirya bai wa mata damar tsayawa neman mukaman siyasa yadda ya kamata ba.
Yaki da cin hanci da almundahana da dukiyar al'umma da gwamnatin Najeriya ke ikirarin tana yi a tsawon shekaru bakwai, bai hana wadannan munanan ayukka gudana ba a sassa daban na kasar.
A Najeriya duk da dokokin kare hakkin kananan yara da aka samar a wasu jihohin kasar, masu ruwa da tsaki wajen kare hakkin yara na ci gaba da nuna damuwa akan yadda ake samun matsalolin.
Mai yiwuwa ana kusa da samun saukin matsalolin da kan haifar da karamcin man fetur a Najeriya, abin da sau da yawa ya kan jefa rayukan jama'a cikin kunci.
Domin Kari