Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Tana Kara Himma Wajen Horas Da Jami'anta


Rundunar sojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana aiki tukuru wajen bin umurnin shugaban kasa na kawar da ayyukan ‘yan ta'adda a ko'ina cikin fadin kasar.

Daga cikin matakan da take dauka akwai horas da jami'anta inda yanzu haka jami'an da ke matakin Saje-Manjo ke kan karbar horo.

Yadda matsalar rashin tsaro ta addabi Najeriya abu ne mai sosa rai wanda ya tayar da hankulan jama'a da dama, kuma baya rasa nasaba da dalilin da ya sa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi ta baiwa jami'an tsaro umurni lokuta daban daban na magance matsalar.

Rundunar sojin Najeirya
Rundunar sojin Najeirya

Bisa ga umurnin da ya yi ta bayarwa da kuma goyon baya da yake baiwa rundunar sojin kasar, babban hafsan mayakan kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya yace rundunar ta mayar da himma wajen horas da jami'anta tare da samar da ingantattun kayan aiki da ke taimakawa wajen samun nasara.

Yace, "kuna gani muna samun nasara don haka dole mu godewa shugaban kasa, da kwarin guiwa da yake bamu wanda ke kara mana azama, yanzu ‘yan ta'adda sun shiga taitayinsu. Yanzu da barayin daji da ‘yan ta'adda da masu garkuwa da mutane basu da maboya domin muna tafe kansu don aiwatar da dokar shugaban kasa ta kawar da su"

Daga cikin matakan da rundunar ke dauka yanzu haka tana kan horas da jami'anta na saje-manjo wadanda ake kira RSM wanda shine horaswa karo na biyu a wannan shekara dake gudana a Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar.

Rundunar sojin Najeirya
Rundunar sojin Najeirya

A hirar shi da Muryar Amurka, babban hafsan mayakan kasa Lt. Gen. Faruk Yahaya yace Saje-Manjo muhimman jami'ai ne wajen koyar da jami'an soji, domin zasu koyar da sauran jami'an soji a barikokin su daban daban musamman ma yanzu da jami'an soji ke ayyuka ko'ina suna cudanya da wasu mutane na daban, hakan zai sa su yi aiki bisa ka'idojin aiki na soji.

A nasa baynin, Auwal Bala Durumin Iya masani kwararre akan harkar laifuka da tsaro yana ganin cewa, yana da tasiri sosai wajen magance matsalar tsaro bisa ganin cewa yanzu akwai sababbin dabaru da ‘yan ta'adda suka fito da su da dole ne sai anyi amfani abubuwa na zamani a shawo kan matsalar da dole ta hanyar horaswa.

Yace wadannan jami'an na Saje-Manjo idan aka horas da su kamar ana aika ilimin ne ga dukanin sojoji domin su ne ke horas da na kasa da sababbi masu shiga soji.

Horas da jami'an da aka yi na farko a jihar Lagos, babban hafsan sojin yace sun ga alfanunsa sosai saboda haka suke sa ran wannan da ake yi a Sakkwato zai kara kawo alfanu ga ayyukkan sojin.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG