Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Najeriya Sun Fara Nuna Fargaba Kan Gwamnati Mai Zuwa


Wasu ‘Yan Najeriya
Wasu ‘Yan Najeriya

Yayin da harkokin siyasa suka kankama gadan-gadan a Najeriya, wasu ‘yan kasar na mamakin yadda gwamnatocin siyasa da suka yi mulki suka kasa warware matsalolin rayuwa ga jama'a, tare da nuna fargabar kada gwamnati mai zuwa ta bi sawun ta baya.

SOKOTO, NIGERIA - Hakan na faruwa ne lokacin da dimokradiyar kasar ta shafe fiye da shekara biyu amma babu wadatar ababen more rayuwa ga talakan.

Yanzu dai a iya cewa hadarin siyasa ya turnuke sararin samaniyar Najeriya, sai dai ruwan wadanda suka gabata sun kasa wanke matsalolin rayuwa musamman haujin wadatar da ‘yan kasa da ababen more rayuwa kamar yadda rahotaani ke nunawa, ko da yake, gwamnatocin sun ce sun yi iya bakin kokarinsu.

Alal misali, idan aka dubi haujin wutar lantarki, fiye da shekara 20 yanzu ‘yan kasa na kokawa akan rashinta kuma har yanzu haka batun yake a mafi yawan yankunan kasar.

Wani dan Najeriya Mukhtar Sani Sanyinna, ya ce lamarin wutar lantarki sai dai hakuri saboda ko yaushe gara jiya da yau,matsalolin da karancin wuta suka kawo ba su ko kirguwa, duk masana'antu da suka durkushe a yankin arewa rashin wuta ya hana sake farfadowa da su.

Wasu ‘Yan Najeriya Sun Fara Fargabar Kada Gwamnati Mai Zuwa Ta Bi Samun Na Baya
Wasu ‘Yan Najeriya Sun Fara Fargabar Kada Gwamnati Mai Zuwa Ta Bi Samun Na Baya

Wani dan Najeriya kuwa mai suna Yusuf Isa jikan Ilah, ya ce karancin wuta ya zama kadangaren bakin tulu ga ‘yan Najeriya, yana mamakin yadda dukan gwamnatoci suka kasa kawo karshen matsalar, duk da bayar da ita ga kamfuna ya kasa inganta samar da wutar ga jama'a.

Har Ila yau wasu ‘yan kasar na ganin duk da yake lamurran siyasa sun kama gadan-gadan, ‘yan siyasa na ta yi wa jama'a alkawura, yanayin kunci da wasu jama'a suka samu kansu ciki na iya yin mummunan tasiri wajen zaben da zai gudana shekarar 2023.

Farfesa Bello Badah na daga cikin masu wannan ra'ayin, inda ya ce a shekara ta 2015, ‘yan Najeriya sun sa rai kwarai da gaske akan cewa shugaban da aka zaba abubuwa za su yi sauki.

Ya kara da cewa, kasafin kudinsa ma na farko ya kwadaitar da jama'a cewa abubuwa za su yi kyau, amma yanzu shekaru fiye da bakwai abubuwa sai kara lalacewa suka yi, lamarin wutar lantarki an kashe makudan kudi ba abin da ya gyaru, zaman lafiya ba abin da ya yi sauki, talauci ba sauki, hakan ya sa jikin jama'a ya yi sanyi akan zaben shugabanni a Najeriya.

Wasu ‘Yan Najeriya Sun Fara Fargabar Kada Gwamnati Mai Zuwa Ta Bi Samun Na Baya
Wasu ‘Yan Najeriya Sun Fara Fargabar Kada Gwamnati Mai Zuwa Ta Bi Samun Na Baya

To da yake ana bisa gabar da za ta kai ga gudanar da zaben sabbin shugabanni, ‘yan kasa ke ganin cewa mafita shi ne jama'a su yi karatun ta-natsu su zabi mutanen kirki, domin nuni ya ishi mai hankali.

Wutar lantarki dai daya ce kacal daga cikin ababen more rayuwa da ya kamata talakan Najeriya ya wadatu da su, sai dai fiye da shekara 20 na mulkin dimokradiya abubuwan sun gagari talaka, kuma ba wanda ya san yadda lamarin zai kasance nan gaba.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Wasu ‘Yan Najeriya Sun Fara Nuna Fargaba Kan Gwamnati Mai Zuwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

XS
SM
MD
LG