SOKOTO, NIGERIA - Kula da tsaftar muhalli dai muhimmin abu ne wajen kare lafiya da kuma rayukan al'umma.
A Najeriya, an jima ana samun rashin rayuka na jama'a da dama sanadiyyar rashin kula da tsafta, kamar daga tsaftar abinci ko muhalli, da yadda ba da jimawa ba aka samu a Jihar Sokoto inda wasu mutane 7 ‘yan dangi daya suka mutu sanadiyar cin wani abinci.
Ko bayan haka, an yi ta samun barkewar cututtuka da ke kisan jama'a da yawa, wadanda ba su rasa nasaba da gurbataccen muhalli.
Irin wannan matsalar a cewar masana tsaftar muhalli da ake kira Duba-gari, da ana karfafa ayyukan su da ana iya kaucewa irin hakan.
Aminu Liman Illela Masani kan tsaftar muhalli kuma mataimakin shugaban kungiyar jami'an kula da tsabtar muhalli ta Najeriya mai kula da yankin arewa maso yamma, ya ce da mahukunta na karfafa gwiwar hukunta mutanen da ke saba dokokin kula da tsabtar muhalli da ana iya kaucewa irin wadannan matsalolin.
Ya kara da cewa, akwai karancin jami'an da ke kula da tsaftar muhalli domin wasu sun yi ritaya wasu sun rasu ba'a maye gurbin su ba, duk da yake ana samun wadanda suka kammala karatun kula da tsaftar muhalli.
Kula da tsaftar muhalli dai na daga muradin karni da kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa kamar Najeriya ke fafutukar ganin an cimma.
Aminu Liman ya ce bakwai daga cikin muradun karni 17 sun ta'allaka ga kula da tsabtar muhalli ta yadda za'a samu muhalli mai tsabta da kaucewa kwayoyin cuta da kan iya yin illa ga rayukan jama'a.
Masana lamurran muhalli na ta'allaka matsalolin da ake samu dake yin illa ga muhalli akan rashin kulawar mahukunta duk da yake suna cewa suna kokari wajen kula da kare muhalli.
Dokta Ayuba Dan Asabe Umar masani akan kare muhalli a Najeriya, ya ce da maganar da gwamnatoci ke yi na kula da muhalli suna yi da gaske da an samu kyautatuwar muhalli a kasar.
Matsalolin gurbacewar muhalli na ci gaba da yin barazana ga rayukan da ke saman doron kasa, abinda kasashen duniya ke ta fafatukar ganin an samu mafita ga lamarin.
Saurari cikakken robot dag Muhammad Nasir: