SOKOTO, NIGERIA - Hakan ya kara zaburar da kokarin dakile matsalolin, kamar wani shirin amfani da matasa da kungiyar matasa mai fafatukar raya yankin Arewa maso Gabas ke gudanarwa a wasu Jihohin Arewa tare da samun tallafin asusun tallafi na duniya dake Geneva kasar Switzerland.
Dubban rayukan jama'a sun salwanta, wasu sun rasa matsugunansu, da asarar dukiya ta miliyoyin nairori a kasar sandiyar rashin tsaro, kuma har yanzu matsalar na ci gaba a wasu sassan kasar duk da kokarin da ake yi na shawo kan matsalar.
Hakan ne ya sa hukumomi da kungiyoyi ke ta fadi-tashi wajen bayar da gudunmuwar neman mafita daga matsalolin.
Yankin arewa maso gabashin Najeriya shi ne ya fara tsunduma cikin wannan matsalar kuma yanzu haka kungiyar matasa mai fafatukar raya yankin ta dukufa ga fafatukar bayar da gudunmuwa don ceto yankunan arewa da matsalolin suka dabaibaice ko wadanda ke kusa da abkawa matsalar, inda take samun tallafi daga asusun tallafi na GCERF dake kasar Switzerland.
Shirin ya kunshi amfani da matasa maza da mata da sarakuna da malaman addini domin gina dabi'ar zaman lafiya cikin zukatan, al'umma wanda kuma wasu ke ganin tunani ne mai kyau.
Mata sun ce sune ma sahun gaba wajen samar da kowane irin ci gaba don haka suna da gudunmuwa da zasu bayar, acewar wata mai fafatukar kyautata rayukan jama'a Aisha Abdullahi.
Jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da shirin ke gudana wanda ake shata zai gudana na tsawon shekaru uku.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir: