Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani 'Dan Sanda Ya Yi Wa Abokin Aikinsa, ASP Shu'aibu Sani Malunfashi, Kisan Gilla


ASP Shu'aibu Sani Malunfashi 
ASP Shu'aibu Sani Malunfashi 

‘Yan Najeriya na ci gaba da yin tsokaci akan bukatar mahukunta su rika sanya ido da tabbatar da yin adalci ga dukkan abubuwan da ke faruwa domin kauce wa ci gaba da haifar da matsalolin tashin hankali a kasar.

SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tuhumar wani jami'in dan sanda da yi wa abokin aikinsa kisan gilla a Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, wanda mako daya yanzu rundunar ‘yan sanda ba ta ce komai a kai ba.

Wani “Dan Sanda Yi Wa Abokin Aikinsa ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Kisan Gilla
Wani “Dan Sanda Yi Wa Abokin Aikinsa ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Kisan Gilla

Ana tuhumar wani dan sanda da aka bayyana sunansa da Abdullahi da yi wa abokin aikinsa, ASP Shu'aibu Sani Malunfashi, kisan gilla kuma kimanin mako daya kenan rundunar 'yan sanda a Jihar Kebbi ba ta ce komai ba a kan lamarin duk da kwanaki da Muryar Amurka ta yi tana tuntubar rundunar ‘yan sandan.

Akan haka ne muka tuntubi dangin marigayin ko yaya suka samu labarin rasuwarsa.

Mahaifinsa, Sani Shu'aibu Malunfashi, wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, ya ce labarin ya zo musu da firgita da tsoratarwa amma zamansu Musulmi sun san cewa ASP Shu'aibu Malunfashi ba zai wuce wannan ranar ba, sai dai yanayin rasuwarsa ne ya tayar musu da hankali.

Marigayi ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Da Mahaifinsa Sani Malumfashi Wakilin Muryar Amurka
Marigayi ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Da Mahaifinsa Sani Malumfashi Wakilin Muryar Amurka
Wani “Dan Sanda Ya Yi Wa Abokin Aikinsa ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Kisan Gilla
Wani “Dan Sanda Ya Yi Wa Abokin Aikinsa ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Kisan Gilla

Ya ce bayanin da suka samu shi ne wani ya je har gidansa ya yi sallama ya shiga ya soka masa karfen da har ya huda zuciyarsa, kuma Allah cikin ikonsa ya sa wanda ya yi aikin ya fada da kansa cewa sun yi fada da ASP Malunfashi kuma ya kashe shi.

A garin na Argungu inda lamarin ya faru jama'a sun nuna alhini domin marigayin mutum ne na kowa a cewarsu.

Yanzu ASP Malunfashi ya bar duniya kuma tuni aka yi jana'izarsa kamar yadda Musulunci ya tanada, amma dai iyali da danginsa na cike da alhinin rashinsa.

Nafisat Shu'aibu Malumfashi, matar marigayin, cikin karyayyar murya, ta ce ba abinda zata fada sai dai Allah ya gafarta wa marigayin.

Wani “Dan Sanda Ya Yi Wa Abokin Aikinsa ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Kisan Gilla
Wani “Dan Sanda Ya Yi Wa Abokin Aikinsa ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Kisan Gilla

Ita ma mahaifiyarsa, Fatima Sani Malunfashi, cikin alhini ta fadi yadda lamarin ya faru kamar yadda mahaifinsa ya fada. A karshe ta bayyana cewa koda ba a soka masa karfen da yayi sanadin rasuwarsa ba, ba zai wuce wannan ranar ba, amma suna rokonAllah ya bi masa hakkinsa domin basu yafe ba.

Duk da yake rundunar 'yan sanda ta ki cewa komai akan batun, mako daya da faruwarsa, dangin marigayin sun ce suna da shaida akan kisan da aka yi wa dansu, kuma daga cikin tarin shaidar akwai kalaman da DPO na Argungu ya furta lokacin da yake zantawa da mahaifin marigayn ta waya.

Jami'in ya shaida wa mahaifin cewa wanda yayi kisan shi ya kawo kansa ofishinsu ya fadi abin da ya faru, kuma shi ma mai mukamin ASP ne.

Yanzu dai iyalan suna karfafa fatan cewa za a yi mùsu adalci.

Saurari cikakken rahoton daga Muhammad Nasir:

Wani “Dan Sanda Yi Wa Abokin Aikinsa ASP Shu'aibu Sani Malunfashi Kisan Gilla.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG