Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata ‘Yan Siyasa Sun Ce Sun Yi Takaicin Sunayen 'Yan Takara Da Hukumar Zabe Ta Fitar


Mata 'yan siyasa
Mata 'yan siyasa

A Najeriya mata ‘yan siyasa sun ce irin sunayen ‘yan takara da hukumar zabe ta fitar ya kara jefa fargaba cikin zukatansu ganin har yanzu ba a shirya bai wa mata damar tsayawa neman mukaman siyasa yadda ya kamata ba.

To sai dai wasu matan suna ganin idan bera da sata ko daddawa da wari.

Mata ‘yan siyasa sun jima suna korafi akan abin da suke kira rashin ba su damar tsayawa takarar mukaman siyasa, har ma sun jima suna daukar matakai amma dai har yanzu kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu.

Sunayen ‘yan takarar da zasu fafata a zabubbukan shekara ta 2023 a Najeriya da hukumar zabe ta fitar, a cewar shugabar zauren mata ‘yan siyasa a Najeriya Barista Ebere Ifendu, ya kara nunawa a fili cewa har yanzu lamarin bai canja ba.

Ta ce idan aka tattara adadin alkaluman ‘yan takarar za a ga cewa daga cikin ‘yan takara dubu hudu da bari biyu, Hamsin da tara dake neman mukamai, kama daga shugaban kasa zuwa ‘yan Majalisar tarayya, mata dari uku da tamanin da daya ne kawai a ciki, wanda ya kama kashi 8.9 cikin 100 na ‘yan karar.

Ta ce ba wai sabon zance ba ne, ko a zabubbukan 2019 adadin mata da aka zaba yana matsayin kashi 4.71% adadinda ta nuna an samu koma-baya daga na 2015 inda aka samu 5.6%.

To wai me yasa kodayaushe Mata ke korafi akan ba'a basu dama a fagen siyasa, duk da cewa akwai su da yawa a wasu bangarorin gwamnati kuma suna bayar da gudunmuwa.

Ubaida Muhammad Bello ita ce shugabar zauren ‘yan siyasa mata a Najeriya reshen jihar Sakkwato.

Ta ce suna ganin ba a basu dama ne, saboda ba su da uban gida a fagen siyasa, kuma su ba wai shugabancin ne suke kwadayi ba sai dai suna son su wakilci ‘yan uwansu mata ne saboda ciyon mace na mace ne, amma sun kasa samun damar saboda rashin fahimta, ko ana ganin basu iyawa ko kuma tasirin addini da al'adu.

Sai dai wasu matan na ganin cewa suma suna da nasu laifi ga koma-bayan da suke samu a fagen siyasa, acewar Nafisa Adamu Gurori wadda ke ayukkan jinkan al'umma inda ta samu damar jin ra'ayoyin wasu wata akan wannan batun.

Tace su kansu mata suna da matsala saboda kishi da suke dashi, macce bata son ta zabi mace saboda tana ganin tana iya kawo mata matsala, ta fi son ta zabi namiji inda take ganin tafi samun biyan bukata.

Damuwa da wannan yanayin duk da fafatukar da ake yi ta neman sauyi, ya sa Zauren mata ‘yan siyasa a matakin kasa, ya gudanar da bincike kuma a karshe ya gano cewa akwai bukatar samun dauki daga sassa daban daban wajen kawo sauyi ga matsalar.

Shugabar zauren tace saboda haka ne suke neman dauki daga sassa daban daban da suka hada da kasashen shari'a, da na zartaswa ‘yan majalisar dokoki, jami'an tsaro da kafafen yada labarai, da dai sauransu.

Duba da cewa wannan korafin ba sabo bane ga mata abin jira a gani ko samun daukin daga hukumomi da sassan da suka nema zai yi tasiri wajen sauya lamarin ko akasin haka.

Saurari rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG