Kasar Burtaniya ta ce za ta taimakawa Najeriya don ganin cewa ta fita daga matsalolin rashin tsaro da suka dabaibaiye kasar musamman yankin arewa.
Wani jirgin ruwa dauke da mutum kimanin 160 ya nutse a garin Warrah dake karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi, lamarin da ya zuwa yanzu ba a san adadin mutanen da suka rasu ba.
Matsalar rashin tsaro a Najeriya na ci gaba da haifar da damuwa da tilasta jama'a daukar matakai koda basu da dadi a rayukan su.
A Najeriya ana ci gaba da samun salwantar rayuka sanadiyar ayukkan ‘yan bindiga lamarin da masana ke kallon cewa shawo kansa ya gagari hukumomi.
Kasar Amurka ta bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ta cutar coronavirus, ba su sa ta karaya ko ja da baya ba ga tallafin da take baiwa kasashen duniya domin kyautata rayukan jama'ar su.
Kungiyoyi agaji na taka rawa wajen samar da makoma ga kananan yara da basu da hanyar samun ilimi.
Yadda ‘yan ta'adda ke nuna gadara wajen kai hare-hare ga jama'a, na tilas ta shugabannin al'umma jaddada kira ga hukuma da ta yi da gaske wajen shawo kan wannan matsalar.
Masana lamurran tsaro na ganin rashin karfafawa hukumomin tsaro a Najeriya na daga cikin abubuwan da ke kawo koma baya ga yunkurin shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar.
Alamu na dada nuna cewa ‘yan Najeriya sun fara kosawa da rashin hukunta wadanda ake kamawa da ayyukan ta'addanci har suna daukar doka a hannunsu.
Masana a Najeriya na ganin ba wani yunkurin samar da ci gaba da zai iya yin tasiri a kasar muddin ba magance matsalar rashin tsaro aka yi ba.
Lamarin rashin tsaro a arewacin Najeriya na ci gaba da daukar sabon salo, inda jama'a ke nuna bukatar daukarwa kan su hukunci.
Alamu na nuna cewa har yanzu ‘yan Najeriya ba su san inda aka dosa ba game da matsalar rashin tsaro, domin duk da matakan da hukuma ke dauka, hakan bai hana wanzuwar ayyukan ta'addancin ba.
Masana kula da lafiya a Najeriya sun bayyana bukatar da ke akwai ta amfani da tsarin binciken kiwon lafiya na hadin gwiwa tsakanin likitocin dabbobi da na al'umma domin saukaka gano cuta da maganin ta.
Bayan kaddamar da mota ta farko da aka hada a Najeriya mai aiki da lantarki yanzu kuma an samar da tashar cajin motar ta farko mai aiki da makamashin hasken rana.
Masana tarihi a Najeriya na ganin cewa idan aka karfafa tare da yin aiki da gudunmuwar da sarakuna ke bayarwa akwai yiwuwar su yi tasiri wajen magance matsalolin da suka dabaibaye kasar.
Tabbatuwar ganin wata a Musulunci shi ke tabbatar da soma kidayar kwanakin watan da kuma soma ibada wadda ake yi a cikin wannan wata na Musulunci.
A Najeriya manoma na ci gaba da kokawa akan yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da gurgunta noman abinci duk da yake gwamnatoci na kokarin karfafa gwiwar manoman don su dukufa ga noman.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta gargadi masu mu’amula da kudade ta na’urar POS, akan su kiyaye ka’idojin mu’amula da kudade ko su dandana kudarsu.
A Najeriya mahukunta a jihar Sakkwato dake arewacin kasar na daukar matakan hana yaduwar wata cuta da ta bulla a makarantar ‘yan mata har ta yi sanadin salwantar rayuwa.
Al'ummomi a arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da zaman zulumi saboda rashin tabbas na tsaron rayukansu, duk da ikirarin da hukumomi ke yi na kokarin shawo kan matsalolin rashin tsaron.
Domin Kari