Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Kula Da Lafiya Sun Bukaci Hadin Gwiwar Likitocin Dabbobi Da Na Al'umma


Masana kula da lafiya a Najeriya sun bayyana bukatar da ke akwai ta amfani da tsarin binciken kiwon lafiya na hadin gwiwa tsakanin likitocin dabbobi da na al'umma domin saukaka gano cuta da maganin ta.

Binciken hukumar lafiya ta duniya ya tabbatar da cewa akwai akalla cututtuka 500 wadanda ke kama jama'a kuma akwai tabbacin cewa daga dabbobi ne suka samo asali.

Wannan a cewar likitoci wasu lokuta akan samu jama'a da wata cuta ayi ta bincike da shan magunguna amma a kasa shawo kan cutar.

Akan hakan ne likitocin ke ganin ya kamata Najeriya ta tafi tare da sauran kasashe a wannan haujin.

Bisa ga lura da cewa ba da jimawa ba ne hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta bayar da bayanin sake bullar cutar murar tsuntsaye a wasu jihohi a daidai lokacin da ake cikin murar mashako ga kuma yawan amfani da shan kayan sanyi da jama'a ke yi musamman masu azumi wanda hakan kan kawo kamuwa da mura ko ya likitocin mutane ke ganin wannan batun na binciken lafiya na hadin guiwa?

Kasancewar akwai cututtuka na mutane da dabbobi masu nuna alamu iri daya likitocin ke shawarar jama'a da kada a rika saurin daukar matakai da zaran an lura da alamar wata cuta domin saurin samu mafita ga matsalar.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG