A jihar Kebbi dake arewacin kasar karshen ‘yan ta'adda sun yi arangama da jami'an tsaro inda kimanin mutane 100 suka rasa rayukan su.
Maharan su kimanin 250 akan babura ne suka dira a garin Makuku dake yankin Sakaba a masarautar Zuru ta jihar Kebbi suka fara satar shanu.
Daga nan jama'ar garin suka ankarar da jami'an tsaro da ‘yan sa kai su kuma nan take suka kai dauki.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta bakin kakakin ta DSP Nafi'u Abubakar ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Karin bayani akan: DSP, jihar Zamfara, jihar Kebbi, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Shima shugaban kungiyar ‘yan sa kai a masarautar Zuru, Mani John ya ce, barayin sun shigo ne daga jihar Zamfara amma dai suma sun sha da kyar a wannan arangama.
Ayukkan ta'addanci dai sannu a hankali suna mamaye sassa daban daban na arewacin Najeriya abinda ke nuna cewa akwai bukatar sake lale domin magance matsalar.
Wata kila taron da shugaban Najeriya yayi da gwamnonin jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro ya buda Sabon babi na sake lalen tunkarar matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Saurare cikakken rahoton a sauti: