Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Ci Gaba Da Tallafawa Najeriya Don Kyautata Rayukan Al’umma


Biden Supermarket Shooting
Biden Supermarket Shooting

Kasar Amurka ta bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ta cutar coronavirus, ba su sa ta karaya ko ja da baya ba ga tallafin da take baiwa kasashen duniya domin kyautata rayukan jama'ar su.

Jakadar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard, ta dukufa ga ziyarar jihohin Najeriya wadanda kasar take hulda da su domin ci gaba da tallafa musu.

An kwashe shekaru masu yawa kasar Amurka ke kawance tare da bayar da tallafi ga Najeriya da ma wasu kasashen duniya domin kyautata rayukan jama'a tare da samar da ci gaba mai dorewa.

A Najeriya, kasar Amurka tana bayar da tallafi a sassa daban daban kama daga sashen kula da kiyon lafiya da ilimi da Noma da makamashi da sauransu, kuma ta kashe makudan kudade a wadannan sassan.

A jihar Sokoto kadai, Amurka ta bada tallafin dala miliyan 122 a fannin kiyon lafiya daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Akan haka ne wakilin Sashen Hausa Muhammad Nasir ya ziyarci wani asibiti da ke samun tallafi daga shirin bunkasa kiyon lafiya na hukumar raya kasashe masu tasowa ta kasar Amurka (USAID) Kuma ya samu ma'aikata bakin aiki.

Domin tabbatar da ayyukan da ke gudana a karkashin kawancen Amurka da Najeriya yadda ya kamata yasa jakadar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, ta dukufa ga ziyarar jihohin Najeriya da zummar karfafa huldar da ke Tsakani, duk kuwa da fama da annobar coronavirus da ake yi.

Amurka dai tana nuna gamsuwa kan yadda gwamnatocin da take hulda da su ke bayar da hadin kai wajen amfanar da al'ummomin su.

Doin karin bayani saurari cikakken rahotan Muhammad Nasir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00


XS
SM
MD
LG