A arewa Maso yammacin kasar ana ta samun ‘yan gudun hijira da wadanda ke rasa rayukan su, sanadiyar wannan matsalar.
Matsalar rashin tsaro a arewacin Najeriya na ci gaba da ta'azzara inda duk safiya sai an samu wadanda suka rasa rayukan su, ko rasa dukiyoyi ko rasa matsugun su.
Bincike na nuni da cewa, a yankin gabashin Sakkwato kowace safiya sai an fuskanci irin wannan matsalar inda talatar nan ma aka kashe wani mai unguwa. Haka lamarin ya ke a yankin Isa inda al'umma ke fuskantar kuncin rayuwa sanadiyar ayyukan ta'addanci.
Irin wadannan matsalolin ne suka sa Dan majalisar dokoki mai wakiltar Sabon Birni ta arewa Aminu Boza wanda ya sha kokawa akan matsalolin ya furta cewa zai aje kujerar sa idan matsalar ta ci gaba haka. Wannan ikirarin yasa jam'iyar sa ta PDP ta gayyace shi akan damuwa da kalaman nasa.
Karin bayani akan: PDP, Sakkwato, Nigeria, da Najeriya.
Masu sharhi akan lamurran yau da kullum na ganin cewa matsalar rashin tsaro ga wuce wani mutum ya ajiye mukaman sa akanta muddin ba gyara aka yi ba.
Yanzu haka dai ‘yan Najeriya ke addu'a tare da zura ido domin ganin yadda yanayin zai kasance domin ana ta daukar matakai ba bu biyan bukata.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: