Masana sun yi misali da noma wanda shine abinda galibin al'ummar kasar su ka dogara wanda ya kasance cike da kalubale na rashin tsaro wadanda ke kawo koma baya.
Ba ga noma kadai matsalar ta tsaya ba domin ayukkan kasuwanci suma sun gurgunta acewar wani wanda ke yankin da ke fama da matsalolin rashin tsaron.
Gurgunta irin wadannan kasuwanni acewar masanin tattalin arziki Bashir Muhammad Achida na jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato abu ne da sannu a hankali zai shafi manyan kamfunna dama arzikin kasa baki daya.
Karin bayani akan: Sokoto, Bashir Muhammad Achida, Nigeria, da Najeriya.
Ba da jimawa ba ne majalisar dattawan Najeriya ta amince gwamnati ta ciwo bashi domin aiwatar da wasu ayukkan ci gaba duk da yake kasa na fama da matsalar rashin tsaro abinda masanan tattalin arziki ke ganin ba lallai ne bashin yayi tasiri ba ga ‘yan kasa.
Masu lura da al'amurra dai na ganin cewa akwai bukatar gwamnati ta kara azama ga magance matsalolin rashin tsaro domin matakan da take kan su a halin yanzu sun kasa biyan bukata.
Saurari cikakken rahoton a sauti: