Sau da yawa gwamnatoci a Najeriya na kaddamar da shirye-shirye na taimakawa manoma domin ba su kwarin gwiwar dukufa ga noman abinci, duk da yake wasu manoman sukan yi korafin cewa wani lokaci ba dukan manoman gaskiya ke samun tallafin ba.
Gwamnatin Sakkwato da ke Arewacin Najeriya ta kaddamar da shirin bayar da tallafin noman rani, inda ta samarda iraruwan shinkafa da takin zamani da maganin kashe kwari da dai sauran kayan noma domin sai dawa manoma cikin rahusa.
To sai dai manoma musamman na yankin gabascin Sakkwato yankin da ya shahara ga noman rani da damina wanda kuma ke fama da matsalar ayukkan ‘yan bindiga, sun ce samar da tsaro a yankin shi ne abu na farko da suke bukata kafin tallafin noma.
Masu lura da al'amurra na ganin cewa muddin ba a magance matsalolin ayukkan ta'addanci akayi ba musamman a yankunan karkara ta yadda manoma zasu samu kwanciyar hankalin yin noman ba, to gurin wadatuwa da abinci zai ci gaba da zama tamkar mafarki, duk da ko makudan kudade da hukumomi ke kashewa sashen noman.
Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Muhammadu Nasir cikin sauti: