Rahoton da Ofishin kula da basussuka ya fitar na kwata na hudu na shekarar 2022 ya nuna cewa jimlar bashin da ake bin Najeriya a wannan lokacin ya haura Naira Triliyan 46.25
A daidai lokacin da ake samun kiraye-kiraye daga Kungiyoyi daban-daban kan shugabancin Majalisar Dokokin Najeriya, a ranar Litinin jam’iyyar APC ta sanar da shiyyoyin da shugabannin Majalisar za su fito.
Akwai Madam Hassana Ayuba Mairiga Tula wacce lauya ce tare da 'yar gwagwarmayar kwato wa mata yanci Hajiya Balaraba Abdullahi, su ma sun yi nazari a wannan shirin.
Ma'aikatar Jinkai da Walwalar Jama'a ta Najeriya, ta yi karin haske kan dalar Amurka Miliyan 1.2 da aka kashe, kan batun samun motocin sufuri don kwashe 'yan Najeriya wadanda yawancin su dalibai ne zuwa gida daga Sudan da ke fama da yaki.
Bankin Duniya ya ce Najeriya na cikin wani yanayi mai rauni tun shekaru biyu da suka wuce, lokacin da aka samu tashin farashin mai a karshen shekara 2021.
Matan sun bayyana tarihin siyasarsu da yawan shekaru da suka kwashe suna gwagwarmaya a wannan fagge da maza suka fi yawa.
Yan Jamiyyar APC mai mulki, da suka hada da shugabani, da Gwamnoni, da jiga jigan jamiyyar, na ta takun saka a kan batun raba manyan mukamai a Majalisar Dokokin Kasa ta 10 mai zuwa, inda batun addini ke neman taka muhimmiyar rawa.
A wannan zango, an ba da shawarar a bi dokokin Allah idan ana so a yi nasara a dukannin fannonin zamantakewa.
Yau shekaru tara kenan da ‘yan ta'addan Boko Haram suka sace dalibai mata su 276 daga makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno, kuma har yanzu ba a san inda ‘yan mata 98 su ke ba.
Manyan yan siyasa da kwararru sun mayar da martani akan bayanan da mai magana da yawun Majalisar Dattawa Ajibola Bashiru ya yi cewa akwai matakai da Uwar jamiyyar APC ta kasa za ta dauka wajen shata shiyoyi da shugabanin majalisar dokokin kasa ta 10 za su fito.
'Yan Majalisar Wakilai da suka samu nasara a zaben wannan shekara na ta yunkurin neman kujerar Kakakin Majalisar, a daidai lokacin da Jamiyyun adawa ke ganin adadinsu ya kai su tsaida wanda zai jagoranci majalisar.
Wani dattijo da ya halarci zaman zauren mai suna Abubakar Adamu, ya amince cewa iyalan mazajen mata da suka rasa mazajensu, ba sa taimakawa marayu da ake barin matan da su.
Hukumar Alhazai ta kasa ta kayyade kudin aikin Hajjin wannan shekarar ta 2023 kan Naira miliyan 2.8 ga kowane maniyyaci, wannan ya bambanta da akalla Naira miliyan 2.5 da maniyata suka biya a shekarar 2022.
Dallar Amurka miliyan 800 da Bankin Duniya ya ba Najeriya domin ta cire tallafin man fetur a tsakiyar wannan shekara, ya jawo cece-kuce tsakanin masana tattalin arziki da masu ruwa da tsaki a kasar.
Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da Ministoci 44 a Majalisar Zartarwa ta tarayya da Gwamnoni 28, za su fara bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu da wa'adinsu zai kare.
Kwararru a fannin shari'a da manazarta a harkokin siyasa, suna ta tafka muhawara akan batun kafa gwamnatin wucin gadi da hukumar tsaro ta farin kaya ta ce wasu suna kokarin yi a Najeriya, duk da cewa babu tanadin yin haka a kundin tsarin mulkin kasar bayan an gudanar da zabe.
Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da ayyuka na musamman ya yi alwashin yin doka da zata taimaka wajen kafa wata hukuma da zata kyautata wa talakawa da masu karamin karfi, to sai dai masana na ganin akwai abin dubawa domin sauran hukumomin da ake da su ba a tafiyar da ayyukansu yadda yakamata.
Bayan kwanaki da kotun koli ta ba da umurni akan tsofaffi da sabbin kudin Naira, gamayyar kungiyoyin marubata kan kare hakkokin bil’adama wato HURIWA, ta yi kira ga shugaban kasa Mohammadu Buhari da ya ajiye aiki.
Wasu ‘yan takarar kujerar gwamna sun bayyana ra'ayoyinsu game da dage ranar zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi, daga ranar Asabar 11 ga watan Maris zuwa ranar 18 ga watan.
Domin Kari