Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RIKICIN SUDAN: Daliban Najeriya Za Su Fara Dawowa Gida A Wannan Makon


Taron Manema labarai Da Ma'aikatar Jinkai Da Walwalar Jama'a Ta Najeriya Tayi Kan Kwaso 'Yan Najeriya Da Ke Sudan 3
Taron Manema labarai Da Ma'aikatar Jinkai Da Walwalar Jama'a Ta Najeriya Tayi Kan Kwaso 'Yan Najeriya Da Ke Sudan 3

Ma'aikatar Jinkai da Walwalar Jama'a ta Najeriya, ta yi karin haske kan dalar Amurka Miliyan 1.2 da aka kashe, kan batun samun motocin sufuri don kwashe 'yan Najeriya wadanda yawancin su dalibai ne zuwa gida daga Sudan da ke fama da yaki.

Babban Sakataren Ma'aikatar Jinkai Dokta Nasiru Sani Gwarzo shi ne ya bayyana wa Muryar Amurka cewa a yanzu haka ana haramar dawo da daliban gida a cikin makon nan mai kamawa.

Wannan yaki da ya barke a kasar Sudan tun ranar 15 ga wanan wata, ya daidaita al'ummar kasar kuma ya shafi dukannin wadanda ke zaune a Sudan, musamman ma dalibai, wadanda suka fito wasu kasashe a ciki har da Najeriya, wanda a yanzu haka ana samun nasara wajen kokarin kwaso daliban, bayan tasgaro da aka samu a wajen aikawa da kudi, da za a yi amfani da shi wajen samo manyan motoci, da za a yi jigilar daliban da su zuwa tudun na tsira kafin jirgin sama ya kwaso su zuwa gida Najeriya.

Sakataran Dindindin Na Ma'aikatar Jinkai Da Walwalar Jama'a Ta Najeriya NASIR SANI GWARZO
Sakataran Dindindin Na Ma'aikatar Jinkai Da Walwalar Jama'a Ta Najeriya NASIR SANI GWARZO

Dokta Nasir Sani Gwarzo shi ne Babban Sakatare a Ma'aikatar Jinkai ya yi karin haske, inda ya ce abin da ya kawo jinkiri har zuwa yanzu shi ne cewa Sudan kasa ce da aka samu matsala wajen aikawa da kudi domin ba su da bankuna masu aikawa da kudade kai tsaye, saboda haka sai an samu wani wanda aka yarda da shi, ko mai sana'ar canjin kudi da zai yarda ya karbi kudi masu yawa ya mika wa wadanda harkar samun motoci ke hannun su.

Sani ya ce ana batun manyan motoci 13 ne kuma kowanen su za a biya dalar Amurka 30,000, saboda haka yawan kudin da hanyar aikawa da shi ne ya jawo tsaiko.

A lokacin da yake amsa tambayar halin da daliban suke ciki ya zuwa ranar Lahadi, bayan sun kwashi kwanaki biyar a wata Jami'a inda aka ajiye su, Dokta Nasiru Sani Gwarzo ya ce Shugaban Kasa Mohammadu Buhari ya sa baki saboda haka an samu izini na a kwashi daliban zuwa kasar Masar, inda ake da jirgin sama kirar C130 yana jira ya kwaso su zuwa gida.

Taron Manema labarai Da Ma'aikatar Jinkai Da Walwalar Jama'a Ta Najeriya Tayi Kan Kwaso 'Yan Najeriya Da Ke Sudan 1
Taron Manema labarai Da Ma'aikatar Jinkai Da Walwalar Jama'a Ta Najeriya Tayi Kan Kwaso 'Yan Najeriya Da Ke Sudan 1

Sani ya ce akwai shirin da ma'aikatar sa ke yi na ganin an hanzarta kwaso daliban saboda hankalinsu da na iyayensu ya kwanta. Sani ya ce da yardar Allah za su kwaso daliban duka zuwa gida lafiya.

Wani dan Najeriya kuma dalibi a Sudan wanda ya ke cikin wadanda ake kokarin kwaso wa mai suna Abdulazeez Abubakar Abdullahi ya tabbatar da tashin daliban daga Jami'ar Afrikiya zuwa iyakar kasar Masar wanda ya ce sun kai su dubu daya.

Abdulazeez ya ce kwanakin su biyar a wannan Jami'ar Afrikiya kafin a kwaso su zuwa iyakar kasar Masar.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG