Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kashe Kashi 96.3 Cikin 100 Na Kudaden Shigarta Da Ta Samu A 2022 Wajen Biyan Basussuka - Bankin Duniya


IMF World Bank
IMF World Bank

Bankin Duniya ya ce Najeriya na cikin wani yanayi mai rauni tun shekaru biyu da suka wuce, lokacin da aka samu tashin farashin mai a karshen shekara 2021.

ABUJA, NIGERIA - A wani rahoto da ya yi wa lakabi da ''Macro Poverty Outlook for Nigeria'' a turanci wanda Bankin ya fitar a wannan wata na Afrilu, ya bayyana cewa Najeriya ta yi amfani da kashi 96.3 cikin 100 na kudaden shigar da ta samu a 2022, wajen biyan basussuka, wanda shi ne ya kawo aka samu gibin kasafin kudi na yau da kullum, ya kara ta'azzara.

Amma ga kwararre a fanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati yana ganin abinda Najeriya ta yi ba daidai ba ne, saboda a ka'ida, bai kamata kasa ta saki jikinta ba, ace za ta kwashi kudaden shiga da ta ke samu har kashi 96 cikin 100 tana biyan basussuka da su.

Mikati ya ce yin haka zai kawo wa kasar koma baya, saboda haka yana ganin, gara kasar ta tashi tsaye wajen samo karin kudaden shiga, ko walau ta yi karin haraji a cikin kasa ko kuma ta fadada hanyoyi wajen kara al'kaluman da ake samu akan kudaden kaya da ake shigowa da su.

Mikati ya ce kashi 7.5 ake biya na haraji, saboda haka ya bada shawarar a daga alkaluman daga 7.5 zuwa ko kashi 15 ko 30 saboda a samu karin kudade, amma a cewan Mikati idan an bar lamarin haka, ba karamin tashin hankali ba ne, wata rana za a wayi gari babu kudin, kuma ba za a ba kasa bashi ba idan ba ta da kudi ko da na lamuni ne.

A nashi nazarin kan wannan rahoto na Bankin Duniya, masanin tattalin arziki Yusha'u Aliyu, ya bayyan lamarin da cewa wanan matsayi da babban bankin duniya ya fada ko ya ayyana ba za a samu akasi akanshi ba, saboda mutane ne wadanda suke bibiyan kasuwanci da mu'amalar kashe kudi ko mu'amalar musayar kudi na kasashen duniya baki daya.

Yusha'u ya ce wanan ba zai zama abin mamaki ba idan Najeriya ta kashe irin wadannan kudade saboda fadin tattalin arzikin kasar da yawan basussukan da aka tara wa tattalin arzikin kasar, wanda ya Kan nuna bayan an debi shekaru ko biyar ko goma ko fiye da haka da aka tsara daidai lokacin da ya kamata a fara biyan basussukan.

Yusha'u ya bada misali da bashin da aka ciwo aka yi hanyar layin dogo wanda aka shimfida daga Abuja zuwa Kaduna, har an kwashi tsawon shekara daya, ba a samu kudin shiga ta wurin ba, saboda 'yan ta'adda sun kama jirgi kuma sun tsayar da aikin, saboda haka dole Gwamnati ta koma wasu fanoni na samun kudi domin ta cika wadanan ka'idoji na biyan wannan bashi.

Shi ma masanin tattalin arziki kuma Malami a Jami'ar Kashere, Dokta Isa Abdullahi yana ganin akwai abin dubawa a wanan lamarin domin wannan abu ne da ke faruwa idan Gwamnati za ta karkare , kuma yana ganin ba daidai ba ne.

Isa ya ce ya kamata Gwamnati ta daidaita da mutanen kasa, wajen kyautata wa kowa. Isa ya ce duk abinda aka yi na cin bashi ko kuma na kwashe kudi a biya basussuka da su cikin kurarren lokaci , zai kara wa Gwamnati mai shigowa nauyi ne, saboda haka da tun wattani uku ko fiye da suka wuce ne ya kamata Gwamnati ta dauki mataki na bin wadannan abubuwa a hankali wajen nuna kishin kasa, ba wai a kurarren lokaci, a ga abinda ba a yi ba cikin shekaru 8, sai a ce za a hanzarta yin su ba.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Najeriya Ta Kashe Kashi 96.3 Cikin 100 Na Kudaden Shiga Da Ta Samu A 2022 Wajen Biyan Basussuka - Bankin Duniya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:19 0:00

XS
SM
MD
LG