Wasu na ganin dole a raba shiya shiya, wasu na ganin gara a bi cancanta, wasu kuma na ganin a bi addini.
A yayin da ake fafatawa a zaben manyan Ofisoshin Majalisar dokokin kasar ta 10, da za a kaddamar a watan Yuni, jiga jigan Jamiyyar irin su Gwamnonin APC sun ce sun fi ganin tsayar da shugabancin Majalisar a tafarkin shiya shiya, duk da cewa Kwamitin ayiuka na kasa na Jamiyyar APC bai fito fili ya baiyana matsayin sa, a game da kasafta yankunan da za a ware ba.
Kwararre a fanin Siyasar Kasa da Kasa Kuma Malami a Jami'ar Abuja Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi tsokaci cewa batun shiya shiya ba abu ne da ke taimaka wa cigaban demokradiya ba, domin ba ya duba cancanta. Bibi ya ce raba mukamai shiya shiya shi ne ya kawo rushewar Jamiyyar PDP a can baya.
Bibi ya ce Gwamnonin APC da ke dagewa a kan karba karba, su sani cewa tana da nata hatsari, kuma ba za ta haifar da da mai ido ba. Amma ga kwararre a fanin zamantakewan dan Adam kuma Malami a Jami'ar Abuja Dokta Abu Hamisu, ya ce yunkurin da Gwamnonin da jigajigan Jamiyyar APC suka yi abu ne mai muhimmanci saboda idan an samu daidaito a mukamai a kasar to za a iya samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Shi ma mai magana da yawun Jamiyyar APC Bala Ibrahim ya amince da bayanan da Dokta Abu Hamisu ya yi cewa kasar dama tana tafiya ne a kan turbar karba karba, kuma yin haka shi ne adalci. Bala ya ce duba da cewa Gwamnonin APC tare da shugabancin jamiyyar da ma jigajigan jamiyyar su ne suka yi tsayuwar daka, wajen ganin mulki ya koma kudu. Bala ya ce kasar tana tafiya ne a daidai kuma haka shi ne adalci.
Gwamnonin APC sun ce ya kamata a bai wa Kudu Maso Gabas ko Kudu Maso Kudu shugabancin Majalisar Dattawa kuma shugaban Majalisar Dattawan ya kasance Kirista, sannan Shugaban Majalisar Wakilai ya fito daga Arewa maso yamma ko Arewa maso tsakiya.
Gwamnoni sun ce kafin a bai wa wata shiya mukami bayan wadannan da suka lisafa, a yi la'akari da irin gudumawar da ta bayar wajen samun kuri'u a zaben shugaban kasa, amma kuma ba zai hana a yi kokarin janyo wani yanki a jika ba. Mata ma sun ce sun zuba ido su ga yadda za a dama dasu a kasafta mukaman.
Ga sautin rahoton Medina Dauda Daga Abuja, Najeriya: