Shugabannin Jam’iyyu 18 na kasa sun yi wani taron gaggawa a Abuja inda suka bukaci hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS da ta hanzarta bayyana sunayen wadanda ke shirin kafa gwamnatin wucin gadi a kasar.
Wannan zama na zuwa ne bayan wata sanarwa da hukumar ta DSS ta fitar, mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta Peter Afunanya, wacce ta ce ta gano wata makarkashiya da wasu 'yan siyasa suke yi ta yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya karan tsaye da nufin kafa gwamnatin wucin gadi a kasar.
Shugaban majalisar ba da shawara ta jam’iyyu da ake kira IPAC, Yabagi Yusuf Sani, shi ne ya jagorancin zaman majalisar, ya ce sun cimma matsayar yin kira da babbar murya ga hukumar DSS da ta hanzarta bayyana sunayen wadanda ake zargin suna shirya wannan makircin tare da daukar mataki a kansu.
Yabagi ya ce abin kunya ne a ce hukumar tsaro irin DSS da ya kamata tana tattara bayanan sirri domin ta mika wa hukumomin tsaro za ta fito da irin wadannan bayanan, kamata yayi a ji cewa ta kama wasu kuma tana daukar mataki a kansu, a cewarsa.
Da yake bayani akan batun, manazarcin harkokin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja Dakta Abu Hamisu, ya ce akwai abin dubawa a wannan batu. Ya kuma ce wadanda suke wannan yunkuri ba su da masaniya a kan abinda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar a game da irin wannan lamari da zai shafi kasa da zamantakewar ta baki daya.
Abu ya ce abin dariya ne a yanzu, a ce bayan an yi zabe har an fitar da wadanda suke ci zabe wasu su kawo wata magana mai kamar almara. Ya kara da cewa duk wanda bai gamsu ba ya je kotu domin nan ne ake warware takaddama irin wannan.
To ko me kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar don irin wannan matsayi na gwamnatin wucin gadi?
Masanin harkokin shari'a Mainasara Kogo Ibrahim Umar, ya ce babu inda kundin tsarin mulki ya yi tanadi a kan gwamnatin wucin gadi ko ta rikon kwarya tun da ba mulkin soja ake yi a kasar ba.
Mainasara ya ce Najeriya kasa ce da ke mulkin dimokradiyya kuma an riga an yi zabe har an bayyana sakamakon wadanda suka ci zabe.
Sashi 64 da sashi na 153 sun ba shugaban kasa hurumin in ya ga alamun baza a iya yin zabe a kasa ba yana iya hada kai da majalisa sai a dauki matakin kafa gwamnatin rikon kwarya ko ta wucin gadi.
Kungiyar gwamnoni ta kasa ta NGF da kungiyoyin fafutukar kwato ‘yancin ‘yan kasa irinsu HURIWA da CISLAC duk sun amince da wannan kira da majalisar bada shawara ta jam’iyyun kasa ta yi wa hukumar DSS a kan kamo wadanda ake zargi da neman kafa gwamnatin wucin gadi a kuma hukuntasu.
Saurari rahoton Medina Dauda: