Tun da aka fara gasar a farkon watan Janairu, babu kasar da ta yi nasara akan Najeriya sai Tunisia.
Matasa da matasan sun koyi sana’o’i irinsu hada man shafawa da na amfanin gida da sauransu.
Ana minti na 66 ne kuma aka ba Alex Iwobi jan kati saboda wata shigar keta da alkalin wasan ya ce ya yi wa dan wasan Tunisia.
A ranar 4 ga watan Disambar 2021, Tanko ya yi garkuwa da Hanifa inda ya kai ta gidansa ya ajiye ta har tsawon mako biyu kafin daga bisani ya kashe ta.
“Wannan dabbanci da rashin imani ne. Na kasa gane yadda mutum mai hankali zai raba yarinya karama da iyayenta tare da kashe ta.” Atiku ya ce cikin sanarwar da ya fitar.
Hukumomin jiha ta Neja sun tabbatar da aukuwar wadannan hare-hare.
A ranar Lahadi za a buga wasan na Najeriya a filin wasa na Garoua da ke Kamaru mai karbar bakuncin gasar.
“Shugaban yana kira ga tawagar ta Najeriya karkashin jagorancin Agustine Eguavoen, da ta ci gaba da taka rawar da ta dara wacce ta yi a matakin rukuni.”
Dan wasan kasar Sadiq Umar ne ya fara zura kwallo a ragar Guinea-Bissau a minti na 56
Shugaban na Najeriya ya yi kira da a kai zuciya nesa ta hanyar rungumar matakan hawa teburin tattaunawa.
Kazalika bikin zai samu halartar wasu shugabannin kasashen nahiyar Afirka in ji sanarwar ta Garba Shehu.
Kididdigar hukumar kwallon kafa ta FIFA ta 2021 ta nuna cewa Ghana ce kasa ta 52 da ta iya taka leda a duniya yayin da Comoros ke matsayin 132.
A wasanta na farko, Ghana ta sha kaye a hannun Morocco da ci 1-0 yayin da ta yi kunnen doki da ci 1-1 da The Panthers of Gabon a ranar Juma’a.
A bara kadai, masana’antar ta rasa jarumai irinsu, Sani Garba S.K, Zainab Musa Booth (mahaifiyar Maryam Booth,) Ahmad Tage, Isyaku Forest da sauransu.
“Mun yi nasarar kama wadannan kayayyaki ne bayan bayanan sirri da muka samu.” In ji Kakakin NDLEA Babafemi.
A ranar Laraba Najeriya za ta kara da Guinea-Bissau duk da cewa ta shiga zagaye na gaba yayin da Sudan za ta fafata da Masar.
Tuni dai abokansa a masana’antar ta Kannywood suka yi ta taya jarumin alhinin wannan rashi ta hanyar mika sakonnin ta’aziyyarsu.
A cewar Zulum, kashi 700 na manoman jihar sun samu damar komawa gonakinsu.
Kamaru dai ta ci wasanninta biyu, inda ta doke Burkina Faso a wasanta na farko a rukuninsu na A.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya da ke kula da sha’anin sojin kasar ya ziyarce shi a Maiduguri.
Domin Kari