An yaye mata da matasa 450 da suka koyi sana’o’in hannu a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Kungiyar Nagari Cooperative Association ce ta yaye matasan marasa karfi kamar yadda wata sanarwa da gwamnatin Kebbi ta fitar a shafin Facebook dauke da sa hannun mai taimakawa gwamnan a fannin yada labarai Yahaya Sarki.
Yayin bikin yaye matasan, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya kwatanta mata da matasa a matsayin ginshikan kowacce al’umma, wadanda suke bukatar tallafi don su cimma burinsu.
“Ginshikin kowacce al’umma ya rataya ne a wuyan matasa, saboda haka wajibi ne gwamnati ta zuba jari a fannin shirye-shiryen da za su amfani matasa da mata, wadanda za su taimaka musu su cimma burinsu.” Gwamna Bagudu ya ce yayin bikin.
Gabanin jawabin gwamna Bugudu, Babbar Sakatariya a ma’aikatar mata da ayyukan al’umma, Hajiya Aishatu Maikurata ta ce gwamnatin ta kashe miliyan 30 wajen yin garanbawul ga wuraren da ake koyon sana’o’in hannu a jihar.
Matasa da matasan sun koyi sana’o’i irinsu hada man shafawa da na amfanin gida da sauransu.