Najeriya ta kara jaddada matsayinta a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka ta AFCON bayan da ta doke Guinea-Bissau da ci 2-0.
Wannan shi ne wasan Super Eagle na uku na kuma karshe a rukuninsu na D inda Najeriya ke jagoranci da maki 9.
Dan wasan kasar Sadiq Umar ne ya fara zura kwallo a ragar Guinea-Bissau a minti na 56 – bayan wata babbar dama da ya zubar
A minti na 75 William Troost-Ekong ya kara wata kwallon bayan wata yankar zilliya ta bajinta da Moses Simon ya yi wa masu tsaron bayan Guinea-Bissau.
An dai dauki tsawon lokacin kafin a tantance wannan kwallo a na’urar VAR mai fayyace abin da ya faru.
Da ma dai Najeriya ta riga ta kai ga zagayen ‘yan 16 tun bayan da ta lalalsa Sudan da ci 3-1 a wasanta na biyu.
A wasan na farko ta lallasa Egypt da ci daya mai ban haushi.
Wadannan nasarori suka ba ta damar darewa saman teburin rukunin na D a gasar wacce aka ake yi a Kamaru a karo na 33 yayin da Egypt ke biye da ita.
A nata bangaren, kunnen doki kawai Guinea-Bissau ta yi da Sudan, wanda ya ba ta maki daya.