‘Yan wasan Comoros sun yi wa takwarorinsu na Ghana wankin babban bargo a wasan da suka kara a rukunin C na gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke wakana a Kamaru.
Kungiyar ta Comoros wacce ake wa lakabi da Les Coelacantes ce ta fara zura wa Ghana kwallo a raga minti hudu kacal da fara wasa ta hannun El Fardou Ben Nabouhane.
Ghana wacce ke matukar bukatar ta lashe wannan karawa ta buga wasan ne da ‘yan wasa goma bayan da aka ba kyaftin Andre Ayew jan katin a minti na 25.
A minti na 61 Ahmed Mogni na Comoros ya sake zura wata kwallo a ragar ta Black Stars, ko da yake, Richmond Boakye na Ghana ya farke kwallo daya a minti na 64.
A minti na 77 Alexander Djiku na kasar Ghana ya kuma narka wata kwallon a ragar Comoros, lamarin da ya kai wasan 2-2.
Sai dai Mogni da ya ci wa Comoros kwallo ta biyu ya sake farka ragar Ghana a minti na 85.
Wannan shi ne karon farko da ksashen biyu suka hadu a gasar ta AFCON wacce ake yi a juko na 33.
Yanzu Morocco ce take jagorantar C da maki 7 sai Gabon da take biye da ita da maki biyar, dukkansu sun shiga zagayen ‘yan 16.
Mai yi wa Comoros ta shiga zagayen na ‘yan 16 idan aka gama tantance sauran kasashen da suka zama fitattu na uku a rukunansu.
Kididdigar hukumar kwallon kafa ta FIFA ta 2021 ta nuna cewa Ghana ce kasa ta 52 da ta iya taka leda a duniya yayin da Comoros ke matsayin 132.