A ranar 5 ga watan Yunin bara, Najeriya ta haramta amfani da dandalin wanda ta zarga da taimakawa wajen ta da husuma a kasar.
Marigayi Lucas kwararre ne fannin sarrafa harshen Hausa. An haife shi ne a Vom da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filaton Najeriya a lokacin da iyayensa suka je aiki a yankin.
Shahararren dan wasan gaba na Liverpool Salah bai tabuka abin kirki ba, sakamakon yadda zaratan ‘yan wasan Najeriya suka rike shi tsawon mintuna 90 da aka yi a wasan.
Karamar hukumar Giwa na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar hare-haren 'yan fashin daji a jihar Kaduna.
“Ban sanar da ‘yan Najeriya ba tukuna domin ina ci gaba da tuntubar mutane domin neman shawara. In ji Tinubu.
Lokaci na baya-bayan da suka kara a shi ne a wasan sada zumunci da aka yi a birnin Asaba a 2019 inda Super Eagles ta doke ‘yan wasan Pharaohs da ci 1-0.
Dangane da jita-jitar da ke cewa ana sulhu tsakaninsa da gwamna Ganduje, tsohon gwamnan na Kanon ya ce babu wani abu kamar haka.
A ranar Litinin Senegal za ta hadu da Zimbabwe, Guinea da Malawi, Morocco da Ghana sai Comoros da Gabon.
"Yin aikin sa’a 6, 7 zuwa 8 kullum a ofis ba wasa ba ne.” Buhari ya ce.
Wannan sulhun na zuwa ne bayan da aka kwashe watanni ana kai ruwa rana tsakanin bangarorin biyu, lamarin da a wasu lokuta ya kai ga fito na fito tsakanin magoya bayansu.
Al’umomin yankin arewa maso yammacin Najeriya sun yi asarar rayuka da dukiyoyi da dama ga ‘yan fashin daji wadanda kan yi garkuwa da mutane su nemi kudin fansa.
Senegal ita ce ta zo ta biyu a wasan karshe da ta buga da Aljeriya a gasar ta AFCON ta shekarar 2019. Aljeriya ta doke Senegal da ci 1- 0 ta lashe kofin.
‘Yan fashin daji kan kwashi dalibai bila adadin su kutsa da su cikin daji daga baya su nemi kudin fansa kafin su sake su.
“Ya kamata a ce na fito na bayyana sakona ta yadda za a fi saurin fahimta," In ji Lukaku.
A tsakanin watannin Yuni da Yulin bara ya kamata a yi gasar, amma annobar COVID ta sa aka dage zuwa bana.
A watan Agustan shekarar 2018, kamfanin na Apple ya taba zama na farko da darajarsa ta kai dalar Amurka tiriliyan 1.
“Tabbas wannan babban rashi ne. Ina Addu’ar Ubangiji Allah ya jikansa ya yafe masa. Allah ya ba shi gidan Aljanna. Ameen.” In ji Atiku.
A minti na 82 dan wasan Wolverhampton Joao Moutinho ya zura kwallo a ragar United a wasan da suka kara a gasar Premier League wanda aka tashi 1-0.
Tofa na daya daga cikin dattawan Arewacin Najeriya da kan fito fili su yi tsokaci kan yadda za a samar da maslaha game da matsalolin Najeriya musamman na arewacin kasar.
A cewar sanarwar, an saka sunan Lookman a jerin ‘yan wasan a mataki na farko, bisa tunanin cewa za a kammala tantance shi kafin a fara gasar ta AFCON.
Domin Kari