Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari, Jonathan Sun Jinjinawa Super Eagles


Buhari, hagu, Jonathan dama (Facebook/Bashir Ahmad)
Buhari, hagu, Jonathan dama (Facebook/Bashir Ahmad)

“Shugaban yana kira ga tawagar ta Najeriya karkashin jagorancin Agustine Eguavoen, da ta ci gaba da taka rawar da ta dara wacce ta yi a matakin rukuni.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba da irin rawar da kungiyar kwallon kafar kasar ta Super Eagles ke takawa a gasar cin kofin kasashen nahiyar ta AFCON da ke wakana a Kamaru.

A ranar Laraba ‘yan wasan kasar suka kammala wasanninsu na rukuni wadanda duk suka lashe.

Najeriya ta lallasa Masar da ci 1-0 a wasanta na farko ta kuma doke Sudan da ci 3-1 sannan ta doke Guinea-Bissau da ci 2-0.

“Shugaba Muhammadu Buhari na yabawa Super Eagles da suka jajirce a gasar AFCON da ke gudana a Kamaru inda suka lashe dukkanin wasanninsu na rukuni, lamarin da ya ba su damar zuwa zagaye na biyu.” Wata sanarwa da kakakin Buhari Femi Adesina ya fitar a ranar Laraba ta ce.

Tun dai a wasan da ta buga da Sudan, Najeriyar ta kai zagayen ‘yan 16 inda a yanzu take da maki 9 bayan ta ka da Guinea-Bissau.

“Shugaban yana kira ga tawagar ta Najeriya karkashin jagorancin Agustine Eguavoen, da ta ci gaba da taka rawar da ta dara wacce ta yi a matakin rukuni.”

Buhari ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa tawagar ta ‘yan wasan Najeriya.

A gefe guda kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, shi ma ya sarawa ‘yan wasan na Super Eagles bisa wannan kokari da suka yi.

“Sannun ku da kokari ‘yan wasan Najeriya na Super Eagles da kuka kai zagayen ‘yan 16 a gasar AFCON 2021 da ke gudana a Kamaru, inda kuka nuna bajinta 100 bisa 100.”

“Wannan wata alama ce da ke nuna cewa Najeriya kasa ce mai jajircewa da samun nasara a ko da yaushe.” In ji Jonathan.

XS
SM
MD
LG