Tsohon mataimakin shugaba Najeriya Atiku Abubakar ya yi kira ga ‘yan wasan Super Eagles da kada su karaya duk da cewa an fitar da su a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Kamaru.
A ranar Lahadi Tunisia ta sallami Najeriya a gasar bayan da ta lallasa ta da ci daya mai ban-haushi a zagayen ‘yan 16.
“Kada mu taba karaya. Ina mai jinjina wa ‘yan wasa da daukacin tawagar kungiyar Najeriya bisa nasarorin da suka samu.
“Mun sha kaye a gasar AFCON 2021 a wannan mataki, amma ya kamata mu mayar da hankalinmu kan wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a Qatar wanda za mu buga da Ghana.” Atiku ya ce.
Tun da aka fara gasar a farkon watan Janairu, babu kasar da ta yi nasara akan Najeriya sai Tunisia.
‘Yan wasan Agustine Eguavoen na Super Eagles sun doke Egypt da ci 1-0, Sudan 3-1 da Guinea-Bissau da ci 2-0 a rukunin D, nasarorin da suka ba su damar shiga zagayen na wasannin kwaf daya.