Batun takaddama tsakanin shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tnubu ke jagoranta da shugabannin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da daukar hankalin masana da masu fashin bakin kan sha’anin siyasa da diflomasiyya.
Rundunar ‘yan sanda jihar Kano a Najeriya ta gargadi masu sha’awar tada fitina a cikin al’uma su sauya tunani, a dai-dai lokacin da tace ta dukufa wajen bankado wadanda keda hannu wajen cinna wuta a sakatariyar karamar hukumar Gwale ta cikin birnin Kano.
Kungiyar masu fiton kayayyaki ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta bude tashar kan iyaka ta Lolo da ke tsakanin Jihar Kebbi da Jamhuriyar Benin.
Ofishin raya kasashe na kasar Burtaniya ta bullo da sabon Shirin bunkasa harkokin noma da cinikayyar amfanin gona, domin tallafawa kananan manoma a wasu jihohin Najeriya, cikin har da jihar Jigawa.
A Najeriya, masharhanta da ke nazari a fagen siyasar kasa da kasa da kuma harkokin diplomasiyya na fashin baki akan koken da kungiyoyi ko jam’iyyun siyasa na kasar ke yi wadanda ke mayar da hannun agogo baya ga ci gaban kasa da nufin neman dauki.
Matasan sun nuna bacin ran su ne game da zargin wani dan sanda da suka ce ya harbe wani dan Uwan su a Unguwar Kurna, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar shi bayan an garzaya da shi Asibiti.
Dubban matasan da suka mamaye babban titin da ke unguwannin Kurna da Rijiyar Lemo, sun hana masu shiga birnin Kano domin kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum.
Masu ruwa da tsaki a fannin Lafiya na Najeriya sun nanata muhimmancin kafa cibiyoyin ba da horo na musamman ga daliban da suka kammala karatun aikin likita a jami’o’in kasashen waje.
Yayin da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ja kunnen masu yunkurin tada fitina a jihar, kwarraru da ke sharhi kan harkokin tsaro sun ankarar da al’umma game da wasu muhimman al’amura da suka shafi shiga cikin harkokin tarzoma.
Kotun Daukaka Kara ta sake jaddada nasarar Gawuna bayan yaduwar wata jita jita.
Fitar da wani sashi na daftarin hukuncin kotun daukaka kara ta Najeriya dake Abuja, dangane da shari’ar zaben gwamnan Kano ya sake dumama yanayin siyasar jihar, dai dai lokacin da masana dokoki da shari’a da kuma manzarta a fagen dimokaradiyya ke bayyana albarkacin bakin su.
Gwamnatin jihar Kano ta jam’iyyar NNPP ta ce za ta je kotun koli, bayan da kotun daukaka kara da ke Abuja ta ce dan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara a zaben gwamnan Kano daya gabata, kamar yadda kotun sauraren kararrakin zabe ta Kano ta yanke hukunci a kwanakin baya.
Yajin aikin da kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta fara a daren jiya litinin ya gurgunta harkokin karatu a makarantun gwamnati na jihar Kano. Makarantun sakandare dana kwalejojin ilimi mai zurfi da kuma Jami’o’i mallakar gwamnatin jihar da na tarayya sun kasance a kulle a yau talata.
Yayin da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya roki Majalisar Dokokin kasar ta shafe dokar da ta bada damar gudanar da zabukan gwamnoni na bai daya a Najeriya, yanzu haka masana dokoki sun fayyace hanyoyin da majalisar ka iya bi domin cimma nasara.
Al’amura sun tsaya cik a majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya tun bayan da ‘yayan kungiyar ma’aikatan Majalisun suka tsunduma yajin aiki a shekaranjiya Litinin. Sai dai masu sharhi na cewa yajin aikin ba shine mafita ba.
Domin Kari