A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Juma'a, mai dauke da sa hannun kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, kwamishin ‘yan sandan jihar ta Kano Mohammed Usaini Gumel ya gargadi magoya bayan jam’iyyun APC da NNPP a jihar Kano da ke kokarin gudanar da wani gangami ranar Asabar, da su guji shirya duk wani taro da rundunar bata amince da shi ba.
Yace doka za ta yi aiki a kan duk wani ko wasu mutane da suka fito da sunan yin wata zanga zanga ko kuma taron jama’a kowane iri ne, yana mai cewa rundunar da sauran jami’an tsaro sun yi tanadi a kan masu kunnen kashi.
Detective Auwalu Bala, kwarrare ne a kan harkokin tsaro da kimiyyar bankado masu kokarin tada fitina a tsakanin al’uma, ya ce akwai bukatar mutane su yi taka-tsantsan wajen shiga duk wani irin taro da aka shirya.
"Akwai abin da masana ke kira mafi karancin ilimi a kan lamuran tsaro, wanda ya kamata ace kowa yana da shi, babba da yaro maza da mata. Wannan ilimin shi zai baka dama ka tantance cewa, me ya kamata ka je ka yi, shin ya kamata ka halarci taron ko kuma a’a, su waye suka shirya taron, me ake so a cimma a wurin taron, da makamantan su,” a cewar Bala.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar al’ummar matasan Yarbawa mazauna Kano ke kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sanya ido sosai wajen tabbatar da zaman lafiya a Kano, a daidai lokacin da ake dambarwar shari’ar zaben gwamnan Kano.
“Zaman lafiyar Kano, saye da sayarwa a Kano, ilimin yaranmu, abin da muke hange kenan. Duk abin da za’a yi, a nemi yanayin da za’a samu zaman lafiya,” a cewar kakakin kungiyar Comrade Taufiq Olalekon.
A halin da ake ciki, ya zuwa yanzu birni da kewayen Kano na cikin yanayin aminci kuma al’uma na ci gaba da harkokin su na yau da kullum.
Saurari rahoton Mahmud Kwari:
Dandalin Mu Tattauna