Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasuwa Za Su Rufe Kasuwannin Arewacin Najeriya


Taron bude tashar kan iyaka ta Lolo dake tsakanin Jihar Kebbi da Jamhuriyar Benin.
Taron bude tashar kan iyaka ta Lolo dake tsakanin Jihar Kebbi da Jamhuriyar Benin.

Kungiyar masu fiton kayayyaki ta Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta bude tashar kan iyaka ta Lolo da ke tsakanin Jihar Kebbi da Jamhuriyar Benin.

Kungiyar ta yi barazanar rufe dukannin kasuwanni a yankin arewacin Najeriya muddin ba a dauki matakin bude bodar ba.

Ta ce matakin gwamnatin Najeriya na rufe tashar na barazanar durkusar da miliyoyin 'yan kasuwa da ke yankin arewacin Najeriya.

Kasuwa
Kasuwa

A taro da manema labarai a Kano shugaban kungiyar Alhaji Muftahu Ya'u yace tashar kan Iyaka ta Lolo ba ta cikin jerin tashoshin fiton kayayyaki na kan tudu da gwamnatin Najeriya ta rufe, la'akari da cewa, wannan tasha ba ta hada kan iya da Jamhuriyar Nijar ba, don haka bai kamata matakin kungiyar ECOWAS ya shafe ta ba.

Ya ce yanzu haka akwai kwantenoni fiye da 700 jibge a wannan tasha ta Lolo makare da kayayyakin 'yan kasuwa kuma wasu daga ciki na dauke ne da kayayyakin da ka iya lalacewa ko lokacin amfanin su ya wuce.

Ya ce ita kan gwamnati na hasarar naira biliyan 13 kudin haraji a kowane wata sakamakon rufe wannan boda ta Lolo.

A cewar, shugaban kungiyar lokaci ya yi da shugabannin arewa , musamman masu rike da madafun iko, gwamnoni yan majalisar dokoki su fito su yi magana a bude wannan bida ta Lolo.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG