Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sandan Kano Na Neman Hadin Kan Kafofin Yada Labarai Domin Tabbatar Da Zaman Lafiya Yayin Shari'ar Kujerar Gwamna


Kwamishinan 'yan sanda jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel zagaye da sauran jami'an tsaro da shugabannin jam'iyyun siyasa a Kano (Hoto: Facebook/Kiyawa)
Kwamishinan 'yan sanda jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel zagaye da sauran jami'an tsaro da shugabannin jam'iyyun siyasa a Kano (Hoto: Facebook/Kiyawa)

Yayin da Kotun Kolin Najeriya ta ce nan gaba kadan zatayi zaman sanar da hukuncin ta akan shari'ar kujerar gwamnan Kano, Rundunar 'Yan Sandan jihar ta nemi hadin kan kafofin yada labarai domin tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a fadin jihar, gabani da kuma bayan sanar da hukuncin.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da Jam’iyyar ta NNPP ne suka shigar da kara gaban Kotun Kolin ta Najeriya suna kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Abuja wadda tace gwamnan bai cancanci tsayawa takarar gwamnan Kano ba a karkashin inuwar Jam’iyyar ta NNPP.

A ranar 13 ga watan jiya, Nuwamba, ne Kotun Daukaka Karar ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta Kano wadda ta soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a watan Satumba saboda tace ta gano an saka masa kuri’un bogi fiye da dubu 165.

Bayan ta saurari lauyoyin bangarorin biyu a zaman ta na yau Alhamis, 21 ga Watan Disamba, Kotun Kolin Najeriyar, karkashin jagorancin Justice John Okoro ta ce wani lokaci a nan gaba zata sanar dasu rana da lokacin da zata yanke hukunci akan wannan takaddama ta kujerar gwamnan Kano.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da rundunar ‘Yan Sandan Kano ke neman hadin kan kafofin labarai domin tabbatar da doka da oda a fadin jihar ta Kano.

Kwamishinan ‘Yan Sanda, Alhaji Muhammad Hussaini Gumel, wanda ya gana da shugabannin kafofin labarai na Kano yace,

“Kotun Koli ta fara sauraron karar zaben gwamnan Kano, mutane a social media suna maganganu da rubuta abubuwa da dama wadanda ba ingantattu ba kuma suke tada hankulan Jama’a. Dangane da haka ne muka ce ba zamu bari wani ya tsinci magana a social media kuma ya je ya yada ta a kafofin labarai da aka fi aminta da su, wato redio da talabijin da kuma jaridu, wadda hakan ka iya haifar da matsaloli na tada zaune tsaye”.

Kwamishinan yace a baya jami’an rundunar sunyi makamanciyar wannan ganawa da shugabanin manyan jam’iyyun dake takaddama da juna akan wannan lamari wato APC da NNPP.

“Munyi haka da shugabannin jam’iyyu (APC da NNPP), mun ja hankulansu akan cewa kada su bar magoya bayan su su zabi tada tarzoma ta zama itace hanyar da zasu sami nasara akan wannan shari’a da ake yi, mun sa sun rubuta yarjejeniyar alkawarin zaman lafiya”.

Alhaji Muhammad Usaini Gumel ya bada tabbacin cigaba da wanzuwar zaman lafiya a Kano gabani da kuma bayan bayyana sakamakon hukuncin Kotun Kolin ta Najeriya.

Wannan hukunci na Kotun Kolin shine zai kawo karshen dumamar yanayin siyasar Kano a wannan lokaci wadda ya biyo bayan takaddamar zaben kujerar gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris din wannan shekara ta 2023 da muke bankwana da ita.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG