Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Makarantun Sakandare A Jihar Kano Na Karuwa - NDLEA


Wasu dalibai masu shan kwaya
Wasu dalibai masu shan kwaya

Hukumar NDLEA mai hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, ta bayyana damuwa kan yadda matasa a jihar Kano ke mayar da magungunan wasu cututtuka a matsayin ababen sanya maye.

Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kwamitin gwamnatin Kano kan yaki da kwacen waya da shaye-shaye ke shirin kama aiki a makon gobe.

Wasu bayanai da hukumar ta NDLEA ta fitar a kwanan nan sun nuna yadda masu ta’ammali da ababen sanya maye ke karuwa, musamman a tsakanin daliban makarantun sakandare a jihar Kano.

A cewar kwamandan reshen jihar Kano na hukumar ta NDLEA, Alhaji Sadik Ahmed, wasu magungunan da likitoci kan yi amfani dasu wajen kula da masu tabin hankali da ciwon kutirta na cikin jerin magungunan da matasa ke amfani dasu domin maye.

Ya ce “kafin likita ya baiwa marasa lafiya wannan magani sai ya raba kwaya daya gida hudu, amma abin mamaki, wani a cikin wadannan matasa leda guda yake shanyewa a lokaci daya”.

NDLEA
NDLEA

Ta yiwu damuwa da wannan yanayi ne ya sanya, gwamnatin Kano ta kafa kwamitin katta kwana wadda ya kunshi jami’an dukkanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile wanna matsala.

Janar Gambo Mai-Adua mai ritaya wanda shine shugaban kwamitin yace, ”an bamu motoci wadanda zamu yi amfani dasu, an kafa kotun tafi da gidanka domin hukunta wadanda muka kama da laifi kuma akwai wadanda zasu rinka bamu bayanan sirri dangane da wuraren da ake hada hadar kayan maye a sassan jihar Kano”.

Sai dai gabanin wannan kwamiti ya fara aiki gadan gadan, hukumar NDLEA tace ta himmatu wajen toshe kafofin da matasan ke samun wadancan magunguna su mayar dasu kayan maye.

Amma dai masu kula da lamura sunce nasarar ayyukan kwamitin zata dogara ne akan goyon bayan da ya samu daga gwamnati, al’umar gari da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma.

Saurari rahoton mahmud Ibrahim Kwari a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG