Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zagar Matasa Ta Kawo Cikas Ga Zirga-Zirga A Kano


Zanga-zangar matasa a birnin Kano
Zanga-zangar matasa a birnin Kano

Matasan sun nuna bacin ran su ne game da zargin wani dan sanda da suka ce ya harbe wani dan Uwan su a Unguwar Kurna, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar shi bayan an garzaya da shi Asibiti.

Matasa sun haddasa cunkoson ababen hawa da haifar da cikas ga zirga-zirgar jama’a akan hanyar shiga birnin Kano daga garuruwan Katsina da Daura, da sauran garuruwan na arewa maso yammacin birnin Kano. Dubban matasan da suka mamaye babban titin dake unguwanni Kurna da Rijiyar Lemo, sun hana masu shiga birnin Kano kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum.

Matasan sun nuna baccin ran su ne game da zargin wani dan sanda da suka ce ya harbe wani dan Uwan su a Unguwar Kurna, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar shi bayan an garzaya dashi Asibiti. Al’amarin ya faru ne biyo bayan sintirin da ‘yan sandan keyi a yankin domin tabbatar da doka da oda sakamakon tarzomar da ‘yan daba suka yi a yankin, a ranar litinin din daga gabata.

Zanga-zangar matasa a birnin Kano
Zanga-zangar matasa a birnin Kano

Matashin mai suna Salisu Rabi’u wanda dan wasan kwallon kafa ne, ya gamu da ajalin sa yayin da wani dan sanda dake cikin ayarin jami’an tsaron dake sintirin kwantar da tarzomar data biyo bayan fadan ‘yan daba, ya harbe shi da bingida. Bayan mutuwar Salisu Rabi’u wani harbin da dan sandan yayi, ya jikkata wasu mutane guda biyu.

Wannan lamari ya harzuka matasan yankin a ranar laraba, inda suka fantsama akan titin Katsina Road domin nuna rashin amincewar su da abin da dan sandan ya aikata, al’amarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa ya kuma dakatar da zirga zirga a yankin.

CP MUHAMMAD USAINI GUMEL
CP MUHAMMAD USAINI GUMEL

Sai dai a wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta Kano ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce kwamishinan ‘yan sanda Muhammad Usaini Gumel ya bada umarnin kama jami’in dan sandan da ake zargin da wannan aika-aika. Sanarwar tace, kwamishinan ya kuma kafa kwamitin da zai gudanar da bincike akan lamarin.

Jami’an tsaro na cigaba da kokarin kwantar da hankalin matasan, bayan tabbacin da hukumar ‘yan sanda ta bayar na gudanar da bincike bisa adalci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG