Samamen jami’an hukumar ta EFCC na da alaka da binciken da hukumar ke yi akan tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.
Matakin ya sanya ‘yan Najeriya tofa albarkacin bakinsu dangane da makomar kima da darajar kamfanonin Dangote da ma kayayyakin da su ke sarrafawa.
Dakta Ghazali Ado Jibrin, masanin tattalin arziki ne da harkokin kamfanoni a Najeriya ya ce, “ba zai shafi sarrafawa da farashin kayayyakin Dangote ba, amma zai iya shafar farashin hannayen jarin kamfanonin Dangote a kasuwar hannun jari”.
Al’amarin dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa, Alhaji Aliko Dangote, mamallakin rukunin kamfanonin na Dangote, wadda ke da rassa a kasashen Afirka fiye da 10, likafar sa tayi kasa ta kasancewa attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka.
Sai dai Dakta Kabiru Sa’idu Sufi, dan kasuwa kuma masanin kimiyyar siyasar tattalin arziki, ya ce “za’a iya cewa lamarin bai zo da mamaki ba", ya kuma alakanta hakan da "la’akari da matsalar tattalin arziki da Najeriya ta shiga da kuma faduwar darajar Naira”.
Baya ga Kamfanin Dangote, kamfanonin fiye da 50 ne dai hukumar ta EFCC ta ce tana bincikar yadda su ka yi ta’ammali da kudin dala da sauran kudadden ketare tsakanin su da babban bankin tarayya CBN a cikin shekaru 10 da su ka gabata.
To ko hakan ka iya ta’azzara makomar tattalin arzikin Najeriya, wadda ke fama da mashahara? Dakta Ghazali ya ce, “ba zai jawo ba, sai dai ace zaya iya haifar wa tattalin arzikin Najeriya tagomashi, saboda za’a nuna cewa gwamnatin Najeriya da gaske take wajen hana almundahana kuma ana nuna cewa ba za’a kyale kamfanoni su yi abin da ba dai-dai ba”.
Amma duk da haka, a cewar Dakta Ghazali, akwai bukatar hukumar EFCC ta fadada irin wannan bincike nata zuwa hukumomin gwamnati masu alaka ta kai tsaye da harkokin tattalin arzkin kasa, kamar hukumar Kwastam da kamfanin mai na kasa NNPCL da sauran su.
Yayin da masana ke ci gaba da mahawara akan wannan batu, hankali ya koma kan hukumar EFCC, domin ganin sakamakon wannan bincike nata akan kamfanoni da kuma tasirin da zai yi ga makomar tattalin arzikin Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna