Manazarta a fagen siyasar Najeriya da ke sharhi kan harkokin dimokradiyyar kasar, sun fara bayyana mabanbantan ra’ayi dangane da kamun ludayin laffuzan ‘yan takara bayan bude labulen fara kamfe da hukumar zabe ta yi na tunkarar babban zaben 2023.
Malaman addinin Musulinci a Najeriya na amfani da tarukan Maulidin Annabi Muhammadu (SAW) dake gudana a garuruwan kasar wajen kiraye-kiraye ga ‘yan siyasar kasar su kiyaye laffuzan su yayin gudanar da gangamin neman kuri’a, tare da jaddada muhimmancin cika alkawari bayan samun nasarar zabe.
‘Yan fansho a jihar Kano sun gudanar da zanga zangar lumana ranar Alhamis domin matsa lamba ga gwamnatin jihar ta biyasu hakkokinsu na ritaya daga aiki, da kuma yadda gwamnatin ke yanke musu kudadensu na wata-wata.
Babbar kotun Kano a Najeriya ta bukaci ofishin jakadancin kasar China a Najeriya ya samar da wanda da zai rinka yiwa Mr Geng Quantrang tafinta a yayin shari’ar da ake tuhumar sa da kisan gilla ga Ummukulsum Sani Buhari kimanin makonni biyu da suka gabata.
Batun kiyaye laffuza da kalamai yayin tallar ‘yan takara na daga cikin muhimman abubuwan da suka mamaye jawaban shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya.
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ambaliyar ruwa da ke ci gaba da barazana a sassan jihar ta lallata dukiya ta fiye da tiriliyan guda.
A cikin shirin na wannan makon magidanta, manoma da sauran talakawa a Jihar Jigawa ta arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan irin asarar da ambaliyar ruwa ke janyo musu a bana.
Gwamnatin jihar Kano tace fannin kiwon lafiyar na jihar na fuskantar kalubalen karancin ma'aikata. Sai dai gwamnatin tace sabbin ma'aikata fiye da 1500 da ta dauka a baya bayan nan na daga cikin matakan warware kalubalen.
Ambaliyar ruwa da ake samu a wasu sassan Najeriya sanadiyyar matsanancin ruwan sama a kasar na ci gaba da mummunan tasiri ga rayuwa al’umr kasar, musamman mazauna karkara.
Kwararru kan halayyar dan Adam da zamantakewa Najeriya da shugabannin addinai da kuma masu rike da sarautu sun yi mahawara kan yadda za su hada karfi da karfe wajen kawar da matsalolin cin zarafin mata da ‘yammata a tsakanin al’umma.
Harkokin tattalin arziki, cinikayya da zamantakewa na ci gaba da gurguncewa a sassan kananan hukumomin dake yankin kudancin Jihar Jigawa saboda karyewar gadojin dake kan titunan yankin biyo bayan ambaliyar ruwa.
A ranar Talata ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol suka kama Mamu a birnin Alkahira da ke Masar, a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa aikin Umrah a kasar Saudiyya tare da ahlinsa.
Dalibai 'yan Najeriya da su ka yi karatu a Jami'o'i daban daban na kasar Sudan sun yi kira ga hukumonin kasar su tabbatar da adalci ga wadanda rikicin kwanakin baya a Lardin Damazin na kasar Sudan ya ritsa da su.
Bayanai da ke fitowa daga kauyen Zarada Sabuwa na karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya, na nuni da cewa wani mutun da ya kashe mahaifi da mahaifiyarsa, na fama da tabin hakanli.
“Da ma mu akidarmu, duk inda za a yi zalunci, babu adalci, babu mu a wurin. Da a ce kawai wata bukatata ce ko bukatar wasu daga cikin wadanda muke shugabanci tare da su, ai da wannan gayyar ta al’umar Kano, da ba su mana biyayya ba.” In ji Shekarau
Gwamnatin jihar Kano a Najeriya za ta kaddamar da wani gawurtaccen shirin kare lafiyar uwaye da jarirai, wanda ya hada da samar da abinci mai gina jiki.
Kungiyoyi da hukumomin Najeriya da sauran cibiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da kokarin lalubo hanyoyin magance kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Al’umomi a garuruwa da kauyuka masu yawa daga kimanin kananan hukumomi goma da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Jigawa na ci gaba da kokawa tare da neman tallaffi daga gwamnati da hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu.
Domin Kari