Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Kano Za Ta Kaddamar Da Gagarumin Shirin Kare Lafiyar Uwaye Da Jarirai.


Maternidad infantil y adolescente en Centroamérica, Guatemala
Maternidad infantil y adolescente en Centroamérica, Guatemala

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya za ta kaddamar da wani gawurtaccen shirin kare lafiyar uwaye da jarirai, wanda ya hada da samar da abinci mai gina jiki.

KANO, NIGERIA - Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kwararraru kan kiwon lafiyar al’umma ke nanata muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla a watanni shida na farkon haihuwar su.

Wata kididdiga da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ta nuna cewa, Najeriya na da 30% na adadin matan dake mutuwa yayin haihuwa da mace-macen jarirai a duniya. A Najeriya kuma, jihar Kano na cikin jihohin dake kan gaba wajen fuskantar wannan matsala.

Sai dai ga alama hukumomin jihar sun himmatu wajen daukar matakan dakile wannan matsala, la’akari da yunkurin gwamnatin jihar na samar da wani daftarin bayanai da ka’idojin samar da abinci mai gina jikin jarirai da mata masu juna biyu.

Hajiya Halima Musa Yakasai dake zaman daraktar kula da ingancin abinci a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce shiri ne na gwamnatin tarayya, wanda aka kaddamar da shi a shekara ta 2018, kana daga bisani aka umarci jihohi 36 na Najeriya su kaddamar da shi su ma.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

A cewar, Dr Ashiru Hamza Mohammed Kodinatan shirin bunkasa lafiyar jarirai da mata masu juna biyu wato Alive & Thrive, ya ce akwai bukatar daukar matakan wayar da kan jama’a game da muhimmacin samar cimaka ga mata da yara, musamman masu juna biyu da kuma jarirai.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar Kano na kuma tsare-tsaren kafa cibiyar kula da yara masu fama da cutar Tamowa, yayin da a hannu guda kuma kwararru kan kiwon lafiya ke jan hankalin hukumomin kan yadda ake shigo da magungunan sanya jarirai kuzari barkatai cikin Najeriya.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Jihar Kano Za Ta Kaddamar Da Sabon Daftarin Samar Da Abinci Mai Inganci Ga Jarirai Da Mata Masu Juna Biyu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG