A cikin watan Yulin da ya gabata ne wata hatsaniyar kabilanci ta wakana a Lardin na Damazin, tsakanin 'yan kasa da mazauna Sudan din 'yan kasashen waje, musamman 'yan Najeriya.
Al’amarin ya yi sanadiyyar lalata dukiyoyin mutane da gidaje da kuma raunata kimanin mutum 10 yayin da wasu mutane uku suka mutu.
A taro da manema labarai a birnin Kano, kungiyar tsaffin daliban ta bukaci gwamnatin Najeriya ta maida hankali wajen kare muradun 'yan kasar dake zaune a ketare.
Mahukuntan kasar Sudan sun taka rawar gani wajen dakile tarzomar kafin ta yadu, amma kungiyar tsaffin dalibai da su ka yi karatu a kwalejoji da Jami'o'in kasar Sudan, ta jaddada bukatar da ke akwai ga hukumomin Sudan su kara kaimi wajen tabbatar da adalci ga wadanda tarzomar ta shafa.
Imam Aliyu Abdulkadir Abdulkadir, Na'ibin Limamin Masallacin Juma’a na Alfurqan a Kano, kuma shugaban kungiyar tsaffin dalibai Yan Najeriya a kasar Sudan, ya ce kungiyar ta damu ainun kan yadda wasu bata gari suka tayar da fitina a Lardin Damazin na kasar Sudan da sunan kabilanci.
Tarihi ya nuna tun kimanin shekaru 70 da suka shude ‘yan Najeriya ke halartar kwalejoji da Jami'o'i a kasar Sudan, domin karatu a fanonin daban daban na rayuwa.
Dakta Umar Datti Abdullahi, na cikin wadanda su ka kafa kungiyar tsaffin daliban shekaru 22 da suka gabata, ya ce marigayi Sheikh Mahmud Abubakar Gumi da Sheikh Na'ibi Sulaiman Wali na cikin rukunin farko na daliban Najeriya da suka yi karatu a Sudan.
Baya ga yunkurin da take game wannan al’amari, kungiyar ta bukaci hukumomin Najeriya su taka rawar da ta kamata wajen kare muradun ‘yan kasar mazauna Sudan.
Domin Karin bayani saurari rahotan Muhamud Ibrahim Kwari: