KANO, NIGERIA - 'Yan fanshon wadanda suka gudanar da zanga zangar bisa jagorancin kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano sun ce akwai ma'aikatan da suka kwashe shekaru biyar da yin ritaya, amma har yanzu ba a ba su hakkokinsu na barin aiki ba.
Jimlar fiye da naira biliyan 36 ne ‘yan fanshon suke bin gwamnatin jihar Kano bashin kudaden gratuti, wato wasu kudade na musamman da akan bai wa ma’aikacin da yayi ritaya daga aiki bayan shekaru 35 yana aikin gwamnati ko kuma ya cimma shekaru 60 daidai a duniya.
Yanzu akwai dimbin ma’aikata da ke dakon hakkokinsu na ritaya a jihar Kano bayan cimma wancan wa’adi na doka, wadanda suka kunshi ma’aikatan kananan hukumomi da malaman makarantun firamare da sauran rukunin ma’aikata a matakin jiha, al’amarin da ya tilasta gudanar da wannan zanga zanga, a cewar shugaban kungiyar ‘yan fansho ta Najeriya reshen jihar Kano Comrade Salisu Ahmed Gwale.
Ahmed yace shekaru shida da rabi kenan aka kwashe ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar Kano ba su samu kudadensu na sallama daga aiki ba, baya ga yanke wani adadi na kudin fanshon wata-wata da ake yi musu.
Kazalika, a cewar shugaban ‘yan fanshon na jihar Kano, yanzu an kwashe shekaru da dama gwamnatin jihar ta ki yi wa ‘yan fansho karin da gwamnatin tarayya ta bada umarni a yi kamar yadda yake kunshe a cikin dokar kwadago ta kasa.
Zanga zangar dai ta wakana ne a karkashin jagorancin kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano. Shugaban kungiyar comrade Kabiru Ado Minjibir ya ce abinda ‘yan fanshon na Kano ke bin gwamnati ya kai fiye da naira biliyan 36, a don haka tilas ne kungiyar NLC ta dafa musu wajen wannan fafutika ta kwato musu hakki.
Shugaban ma’akatan gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Bala ne ya karbi koken ‘yan fanshon a madadin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, kuma yayi alkawarin cewa gwamnati zata dauki matakan da suka dace domin warware wannan matsala.
A yayin zanga zangar dai wani dan fansho ya yanke jiki ya fadi kuma nan take aka kai masa agajin gaggawa.
Hakan dai wata alamace da ke kara tabbatar da halin damuwar da ‘yan fanshon na jihar Kano ke ciki.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari: