Wata kiddiga da hukumomin lafiya na jihar suka fitar ta nuna cewa, la'akari yawan al'uma kimanin miliyan 20, jihar Kano na bukatar ma'aikatan lafiya fiye da dubu 20 wadanda suka hada da likitoci da ma'aikatan jinya da ungozoma da kwararru kan harkokin gwaje gwajen kimiyya a asibitoci da cibiyoyin shan magani na sassan jihar.
A hirar shi da Muryar Amurka, Dr Tijjani Hussaini sakataren zartarwa na hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko ta Kano, yace matasa fiye da 1500 da aka baiwa takardun aiki wani mataki ne na magance matsalolin karancin ma'aikatan lafiya, musamman a yankunan karkara.
Haka dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake gudanar da bikin makon lafiya na jihar Kano, inda ake bitar nasarori da kalubalen da ayyukan kiwon lafiyar jama'a a jihar ke fuskanta.
shi ma a nasa bayanin, Kwamishinan lafiya na Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, yace baya daukar ma'aikata batun wadata cibiyoyi da asibitoci da kayayyakin aiki da kuma samar da yanayin da ya dace na cikin al'amura da suka sanya a gaba.
Wasu daga cikin matasan da aka dauka aiki bayan shafe shekaru suna aiki kyauta sun bayyana farin ciki tare da alkawarin yin aiki tukuru.
Tuni dai masu sharhi a fannin kiwon lafiya suka fara bayyana cewa, akwai bukatar hukumomi a Najeriya su kara kaimi game da lamuran kiwon lafiyar 'yan kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: