Hakan dai na zuwa ne adai-dai lokacin da wadanda ambaliyar ta ritsa dasu ke neman tallafi daga cibiyoyi, kungiyoyi da hukumomin bada agaji.
Baya ga lalata dukiya, ambaliyar ta yi sanadin mutuwar mutane 134 tare lalata hanyoyin mota 22 da gadoji 11, kamar yadda Mataimakin gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya sanar, yayin karbar bakuncin shugabannin asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya a Dutse.
Ya ce ambaliyar ta shafi a kalla mutane fiye da dubu metan, daga cikin wannan adadi dubu 76 sun rasa matsugunnansu.
Yanzu haka dai al’umar kauyuka da garuruwa a yankin gabashin Jigawa wadanda galibin su ke zauna a sansanonin gudun hiijira da iyalan su, na ci gaba da neman dauki daga hukumomi da kungiyoyin bada agaji na ciki da wajen Najeriya.
Malam Umaru Haruna, jagora a sansanin Rigar Ila, inda aka tsgunar da wadanda ambaliyar ta tasa daga garuruwan su a lardin Hadejia na gabashin Jigawa, yace akwai fiye da mata da yara kananan dubu daya a sansanin kuma suna kokarin samar da abinci da magunguna a gare su.
Yanzu haka dai kananan kungiyoyi, irin su kungiyar matasa ta Muryar Hadejia sun fara kai kayayyakin agajin kayayyakin bukatu ga wadandannan mutane, inda har-ma Malam Umar Nuhu wakilin Bulaman Kubayo ya bayyana farin ciki game da wannan abin kirki, yana mai kira ga sauran al’uma da hukumomi su ceci rayuwar data iyalan su.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin jihar Jigawa ba ta kai ga bayyana irin tallafin data baiwa ko zata baiwa wadanda al’umomi da ambaliyar ta shafa ba, al’amarin daya sanya ‘yan kishin kasa irin su Hon Nasiru Garba Dantiye ke cewa, hakan na nuna yanayi a halin ko in kula daga mahukuntan gwamnatin Jigawan, musamman gwamnan jihar, wanda rahotanni suka ce ya shafe makonni baya jihar.
Yace wannan lokacin da al’umar Jigawa ke neman tallafin gaggawa da kuma kulawa daga shugabanni, la’akari da yadda ambaliyar ta shafe kannanan hukumomi 22 daga cikin 27 na fadin jihar ta Jigawa.
Rahotanni daga lardin Hadejia na gabashin Jigawa na nuni da cewa, jama’ar yankunan kananan hukumomin Kirikasamma da Birniwa na ci gaba da zaman dar saboda barazanar hari daga ambaliyar Kogin Hadejia.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari: