Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tabka Asarar Dukiyoyi Da Rayuka A Ambaliyar ruwan Jigawa


Ambaliyar Ruwan Jigawa.
Ambaliyar Ruwan Jigawa.

Al’umomi a garuruwa da kauyuka masu yawa daga kimanin kananan hukumomi goma da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Jigawa na ci gaba da kokawa tare da neman tallaffi daga gwamnati da hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu.

NIGERIA: Mamakon ruwan sama, kamar da bakin kwarya da aka rinka samu cikin makon da ya gabata a sassan Arewacin Najeriya shi ne musabbabin ambaliyar da ta wakana a jihar ta Jigawa wadda ta lalata kayan amfanin gona da gidaje har-ma da rasa rayukan mutane a wasu Kauyuka da Garuruwa na jihar.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar mutane fiye da 10 sanadiyyar wannan ambaliyar, yayin da dinbin mutane maza da mata ne suka kaura zuwa wasu garuruwa da gine-ginen gwamnati.

Malam Mohammed Hassan na yanki karamar hukumar Hadejia shi ne mutumin da ya rasa ‘ya'yansa uku a lokaci guda bayan da ginin dakin da suke ciki ya rufta akan su sanadiyyar ambaliyar, ya ce ya zuwa yanzu bai kai ga samun tallafi ba, a don haka sai ya yi kira ga gwamnati da cibiyoyin agaji su tallafa wa rayuwar sauran iyalan sa.

Ambaliyar Ruwan Jigawa
Ambaliyar Ruwan Jigawa

Rahotanni daga jihar sun ce daruruwan gidaje a kauyuka da dama suka rushe baya ga gonakin noma na dubban eka a fadin jihar ta jigawa, al’amarin da ya sanya wadanda waki’akar ta auka wa ke neman tallafi daga hukumomi da kungiyoyi.

Musa Hassan Gamji, daga Karamar Hukumar Kafin Hausa, ya ce suna cikin zullumi, saboda ambaliyar ta tagayyara musu muhalli baya lalata amfaninsu na gona, a don haka ya bukaci tallafi daga hukuma da kuma daidaikun mutane.

A nasa bangaren, Malam Usman dan shekaru 70 a duniya shi ne Maigarin Kauyen Tandannu a yakin Hadejia ya ce kayan abincin da na kwaciya, kamar taburmi da katifa da barguna na daga cikin ababen da jama’ar sa ke bukata da gaggawa.

A yayin da ya kai ziyarar jaje ga Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje, gwamnan Jigawa Badaru Abubakar ya yi alkawarin tallafa wa wadanda wannan waki’a ta shafa. Ya ce gwamnatinsa ta sayo injina da motocin yashe magudanan ruwa, musamman hanyoyin ruwa na kogunan Hadejia zuwa Yobe, da nufin dakile wannan ambaliya da kan wakana a duk shekara. Gwamnan ya ce za su kuma gyara magudanan ruwa na cikin garuruwa. Wannan ambaliya da kan wakana a Jigawa duk shekara, wadda ta fi kamari a yankin Hadejia, ta fara haifar da tunani da mahawara a tsakanin kwararru da mahukunta kan duba yuwuwar sauya wa garin Hadejia matsuguni domin kubutar da rayuka da dukiyoyin al’umma.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG