A cigaba da samun 'yan Najeriya masu kokarin ganin an zauna lafiya tsakanin al'ummomi daban daban, wata Musulma ta agaza wa mata Kirista mabukata.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaddamar da taron yakin neman zaben ta na Arewa maso yammacin Najeriya.
Ganin yadda aka fara samun matsaloli a wasu wuraren yakin neman zaben jam'iyyu ya sanya hukumar wanzar da zaman lafiya ta jahar Kaduna da hadin gwiwar wasu kungiyoyi, kiran taron masu ruwa da tsaki don gudanar da yakin neman zabe, da kuma zabubbuka lafiya a fadin jahar.
Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sun ce matsalar tsaro da talauci su ne manyan matsalolin da su ke sa ake aurar da yara da wuri da kuma cin zarafin yara mata a yankin.
Ganin yadda ake yawan samun rahotannin aikata fyade a wasu sassan Jihohin Arewacin Najeriya ya sa gwamnatin jihar Kaduna fito da wani tsarin jadawalin masu aikata fyade don fallasa su a duk inda su ka shiga da nufin kawo karshen wannan ta'annati a tsakanin al'umma
An sake arangama tsakanin 'ya'yan kungiyar Ansaru da kuma 'yan-bindiga a yankin Damarin karamar hukumar Birnin Gwari sakamakon da aka kashe 'yan bindiga biyar.
A yayin da majalissar dinkin duniya ta ware ranakun 13 zuwa 16 a matsayin makon fahimtar juna tsakanin mabanbanta addinai da kabilu, malaman addinin Kirista a jahar Kaduna sun karrama wani matashi da ya haddace al-qur'ani.
MANUNIYA: Matsayin Shugabannin Fulanin Najeriya Game Da Zaben 2023, Nuwamba 11, 2022
Taron yakin neman zaben ‘dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP a Jihar Kaduna ya yi karo da tasgaro biyo bayan afka wa taron da wasu matasa dauke da makamai su ka yi inda su ka jikkata wasu mahalarta taron, to sai dai kuma wannan bai hana taron ba.
Hadakar kungiyoyin arewa shida da su ka gayyaci 'yan-takarar shugaban Kasa na Jam'iyyu sun karkare taronsu karon farko inda su ka rufe da Sanata Bola Ahmed Tinubu na Jam'iyyar APC da kuma Peter Obi na Jam'iyyar Labour.
Jami'an tsaro sun ce har yanzu suna kan kai hare-hare kan 'yan-bindigan da su ka addabi yankunan Arewa maso yamma kuma a nan ne su ka sami nasarar kashe kasurgumin dan-bindigan nan, Ali Dogo da aka fi sani da Yellow
Domin Kari